MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: INA DA BURIN AURE LOKACI NAKE JIRA-Inji Jaruma Nafisa Abdullah

                  Ina Da Burin Aure Lokaci Nake Jira-Inji Jaruma Nafisa Abdullah

Nafisa Abdullahi ta ce tana da burin yin aure kamar kowanne mutum kuma nan gaba masoyanta za su sha labari

Jarumar ta bayyana hakan ne a wani hira da ta yi BBC – Shahararriyar jarumar dai ba ta bayyana takaimaiman lokacin da za ta yi auren ba

Shahararriyar jarumar nan ta dandalin shirya wasan Hausa, Nafisa Abdullahi ta ce tana da burin yin aure kamar kowanne mutum kuma nan gaba masoyanta za su sha labari,jarumar ta bayyana hakan ne a wani hira da ta yi BBC.

Nafisa wacce tauraronta ke kan haskawa a masana’antar fin din ta fito a fina-finai da dama, sannan kuma tana daya daga cikin jarumai masu farin jini sosai.

Jarumar dai ba ta bayyana takaimaiman lokacin da za ta yi auren ba sai dai ta ce, “Aure kamar yadda nake fada kullum lokaci ne na ubangiji, amma kuma hade da niyya, ina da niyyar a raina amma lokacin nake jira.”

Da aka tambaye ta mene ne sunan tauraron kuma ko daya ne daga cikin jaruman fim, sai ta yi dariya kuma ta ba da amsa kamar haka: “Ba shi da suna. Mai rabo ne kawai yana gefe.”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-08 — 8:46 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme