MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: DALILIN DAYASA NA JAWO MATA TA HARKAR FIM-Inji Jarumi Haruna Talle Maifata

Dalilin Dayasa Na Jawo matata harkar fina Finan hausa-Jarumi Haruna Talle Maifata.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Haruna talle maifata jarumi ne kuma babban daraktan kamfani shirya fina finan hausa na maifata movies,haifaffen garin jos ne dake jihar filato.

Jarumin ya bayyana matukar sha’awar sa ga sana’arsa  inda  har ta kai ga jawo matar sa cikinta.

Da yake amsa tambaya akan ko yana fuskantar kalubale tsakaninsa da matar sa a kan harkokin sana’arsa,maifata ya amsa da cewa akwai jituwa yarda da fahimtar juna tsakaninsa da matar sa.

Haruna Talle Maifata ya cigaba da cewa…

“ Bari na fada maka wani abu.gidana babba ne akwai dakuna da yawa wani lokacin anan nake saukar jarumai mata idan a Jos ne nake shirya fin,matata bata taba yin korafi da hakan ba,sai ma ita da kanta da take dafa masu abinci,akwai fahimtar juna tsakanina da matata,ta yarda dani kuma tasan bazan iya cin amanar taba.

Bari ma na fada da bakina cewar nine na jawo matata cikin harkar fim,na bata kudin data dauki nauyin shirya fina finai har guda biyu kuma na kawo ta kannywood ne domin muna mata irin ribar da ake samu a harkar sannan tasan babu wani abu da nake boye mata,kamar yadda jarumin ya bayyanawa jaridar Daily trust a yayin da wata hira da akayi dashi”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-08 — 9:24 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme