MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: BABU KAMSHIN GASKIYA GA MASU YIWA MASANA’ANTAR HAUSA FIM GUGAR ZANA-Inji Ali Nuhu

Jarumai sunyi tsokaci game da zargin da ake ma masana’antar

Ali Nuhu yayi watsi da zargin

Tun ba yauba ake zargin yan fim na kannywood da yin lalata a masana’antar har ma wasu na ganin suna gurbatar da tarbiyar al’umma.

bugu da kari wasu kuma na kallon masu yin fina-finai a matsayin masu aikata miyagun aiyuka irin su zinace-zinace da luwadi da dai sauran su.

A bisa rahoton da BBChausa ta fitar wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na masana’antar kannywood sunyi tsokaci game da wannan zargin da ake masu.

Wannan batun ya fitowa bayan kama wani babban furodusa Harvey Weinstein da aka yi a masana’antar Hollywood dake nan Amurka da yin lalata da wasu manyan fitattun jarumai.

Mai shirya fina-finai a masana'antar Hollywood da aka kama da laifin yin lalata da jarumam masana'antarMai shirya fina-finai a masana’antar Hollywood da aka kama da laifin yin lalata da jarumam masana’antar

Cikin fittatun jarumai da ke zargin sa da yin lalata akwair Angelina Julie da Gwyneth Paltrow da sauran su.

Bisa ga wannan labari gidan jarida suka tada batun wanda tunba yau ba ake zargin yan masana’antar Kannywood da aikata makamanci haka.

Jaruma Hauwa Waraka tana cewa “Ni dai babu wanda ya taba bukatar na yi lalata da shi kuma ban san wata da ta ce wani ya taba son yin lalata da ita ba. Sai dai ka san wannan harkar kowa da halinsa ya zo, babu wanda za ka bayar da shaida a kansa”

 

Ta kara da cewa “Su matan da suke indostri din ai ba yara ba ne, ba yadda za a yi a ce za a kama a neme su da karfi, dole sai sun yarda, don haka duk abin da ki ka ga an yi a harkar nan mutum shi ya so”.

shima fitaccen jarumi Ali Nuhu yayi watsi da wannan zargin inda yake cewa;

 “Ni gaskiya ba taba samun wacce ta ce an yi lalata da ita kafin a sa ta a fim ba, kuma ina ganin wannan zargi ba gaskiya ba ne domin kuwa mu muna kokarin kare addini da al’adunmu ne. Akwai kwamiti da ke sanya ido kan masu neman yin lalata da ‘yan fim da ma kula da yadda muke harkokinmu”.

Babban direktan masana’antar kanyywood Mallam Aminu Saira ya shaida cewa shi bai taba neman yin lalata da wata kafin ya sanya ta a fim.

Direka Aminu SairaDireka Aminu Saira

“Wannan batu ba gaskiya ba ne; hasalima wanna ne karo na farko da aka yi min irin wannan tambayar kuma ina gani da a ce ana samun irin wannan lalata da ‘yan matan fim da suka gabata sun yi korafi. kar ka manta wasu ‘yan fim mata sun yi aure. Da a ce haka batun yake da idan wasu sun yi shiru, wasu sai sun yi magana” cewarsa.

Lamarin da ya faru shekarun baya inda aka samu bidiyon inda ake lalata da wata yar fim ya sanya wa sauran bakin jini har ma a wancan lokaci gwamnatin jihar ta dakatar da yin fim a jihar.

Daga @Pulse Hausa.Com

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-10-18 — 5:06 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme