MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: BA DUKA ‘YAN FIM MATA KE MADIGO BA-Inji Jaruma Hauwa Wraka

Dandalin Kannywood: Ba duka yan fim mata ke madigo ba – Hauwa Waraka.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Fitacciyar jarumar wasannin Hausa na masana’antar Kannywood din nan mai suna Hauwa’u Abubakar wadda aka fi sani da Hauwa Waraka ta bayyana cewa ba fa dukan su ne matan dake sana’ar fim ke yin madigo ba.

Jarumar ta yi wannan karin haske ne a yayin wata fira da tayi da majiyar mu lokacin da aka jefa mata tambaya tayi tsokaci game da zarge-zargen da ake yi musu na aikata laifukan luwadi da madigo a tsakanin su.

Dandalin Mujallarmu.com ta samu dai cewa jarumar tace kwarai akwai masu aikata masha’ar a cikin su amma ba yana nufin dukkan su haka suke ba. Ta ce: “kamar yadda akwai su a cikin ko da Malaman addini amma bai kamata a yi mana kudin-goro ba.” Jarumar ta kuma roki jama’ar gari masu kallon su da su rika yi masu uzuri akan al’amuransu kasantuwar su ma mutane ne kamar kowa.

Da aka tambaye ta kuma maganar aure sai jarumar ta fada cikin raha cewar ita duk wanda ma ya amince zai aure ta to a shirye take tayi masa lefe kyauta.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-09-05 — 6:14 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme