MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: AN YANKEWA WATA TSOHUWAR ‘YAR FIM HUKUNCIN RATAYA SAKAMAKON KASHE SAURAYIN TA DA TAYI

Wata tsohuwar yar Fim din Hausa Rabi Isma’il data taba tserewa daga gidan yarin garin Hadejia na jihar Jigawa a ranar 16 ga watan Disambar 2011 ta shiga hannu.

MARUBUCHI:-yusufkalamuwaheed.

Ita dai Rabi Isma’il an yanke mata hukuncin kisa ne a ranar 5 ga watan Janairun shekara 2005, amma sai aka jefar da ita a gidan yarin Hadejia, inda daga nan ne ta tsere, sai dai a jiya ne jami’an tsaron sirri tare da hadin gwiwar ma’aikatan gidan yarin suka sake shako wuyanta.

Yayin rikicin shari’ar nata har sai da aka kai ga kotun koli, wanda ita ma ya tabbatar mata da hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe saurayinta da tayi mai suna Auwalu Ibrahim ta hanyar bashi kwayoyi, sa’annan ta nutsar da shi duk wai don ta gaji kadararsa.

Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta kasa ya yaba da hadin gwiwar da jami’an tsaron sirri dana Yansanda suka basu don kamo Rabi, daga nan sai ya roki jama’a da su dinga jiyar da jami’an tsaro bayanai kan duk wasu miyagun mutane da suka sani.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-05-31 — 4:46 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme