MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: AN SAMU SABANI TSAKANIN NAFISA ABDULLAHI DA JARUMA HADIZA GABON-Karanta Kaji Dalili

Shahararren jarumar fina finan hausa Nafisa Abdullahi ta tabbatarwa da duniya sabanin dake tsakaninta da jaruma Hadiza Gaborn.

Daya daga cikin manyan fuskoki da ‘yan kallo suka saba gani a masana’antar kannywood wato Nafisa Abdullahi ta tabbatar da sabanin daya shiga tsakanin da jaruma Hadiza Gaborn a kwanaki baya.

Jarumar dai ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da ma’aikatan BBC kai tsaye daga dandalin sada zumunta na zamani  facebook.

Rahoton da Majiyarmu ta Dandalin Mujallrmu ta samu ya nuna cewa duk da jarumar bata amsa tambaya game da abinda ya janwo rashin jituwa a tsakanin su ba acikin firar da akayi da ita,amma tace abu ne daya faru kusan shakara daya da rabi kuma ya riga ya wuce kuma bata son sake dauko wannan zancen.

A shekarar 2017 ne wasu fitattun jaruman kannywood guda biyu sunyi fada inda rahotanni suka tabbatar da cewa harda duka acikin fadan a yayin da ake shirya wani film.

Nafisa Abdullahi ta kara da cewa babu wata dangantaka dake tsakaninta da Hadiza Gaborn,bayan an tambayeta ko suna kiran juna a waya.

Sai tace…

“Bamu cika haduwa da Hadiza Gaborn ba,idan mun hadu muna dan gaisawa”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-05 — 9:57 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme