DANDALIN KANNYWOOD: ALI NUHU YA BAYYANA DALILIN DAYASA YA FARA SHIGA SHIRIN BARKWANCI-Karanta Kaji

Dandalin Kannywood:  Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Dalilin Dayasa Ya Fara Shiga Shirin Barkwanci A Masana’antar Kannywood

Fitaccen jarumin nan, mai bayar da umurni, mai shiryawa da kuma koyar da rawa a

masana’antar fina-finan Hausa da ya dade yana haskakawa ya fito ya bayyanawa duniya
dalilin da yasa yanzu ya tsunduma sosai cikinharkar fina-finan barkwanci da a da ba
kasafai yake yin su ba.

jarumin dai ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin hakan ne domin ya fito ya bayar da gudummuwar sa a wannan bangaren sannan kuma ya sake fuskantar wani sabon kalubalen don kuwa ya gaji da yadda ya dauki tsawon lokaci yana fitowa a matsayin saurayi yana ta tikar rawa.
Daga Mr.Arewa@Arewa Blog.Com

This website uses cookies.