MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: A KARON FARKO FIM DIN RAHAMA SADAU RARIYA YA LASHE KYAUTAR AWARD NA FINA FINAI A SHEKARAR 2017-Karanta Kaji

Rahama Sadau ta yi zarra: Tashin farko, Rariya ya kere ma Mansoor, Dan Kuka da Zinaru a masana’antar Kannywood

Fitacciyar jarumar Fim din nan da aka sallama daga Kannywood, Rahama Sadau ta kafa tarihi, inda tashin farko, Fim din yayi suna tare da karbuwa a masana’antar Kannywood.

Jaridar Pulse ta ruwaito Fim din na Rariya ya kayatar da yan kallo sosai da sosai, har ma ya tsere ma manyan Finai finai da aka fitar a wanann shekara kamar su ‘Yar Fim’, ‘Mansoor’, Dan kuka’ da Zinaru.

 

Dandalin Mujallarmu, ta ruwaito Fim din na Rariya an gabatar da shi ne a ranar 26 ga watan Yunin bana, inda aka kalle shi a garuruwan Abuja da Kano, hakan yasa yan kallo suka dinga shaukin fitarsa gaba daya.

 

Hoton Shi dai Fim din Rariya ya kunshi jarumai kamar su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Hafsat Idris, Fati Washa, Maryam Booth da sauransu, sa’annnan Yaseen Auwal ne ya bada umarnin.

An shirya Fim din ne da nufin fadakar da al’umma kan sauyin da zamani ya kawo, musamman a jami’o’i, ta irin kayan da ake sawa, da kuma rayuwar karya da wasu daliban ke yi.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-10-18 — 12:32 pm

2 Comments

Add a Comment
  1. shema'u salis dirimin iya

    masha Allah

  2. Hakan nanufin rahama sadau tadawo firml kenan?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme