MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: A Karon Farko An Samu Mace’Yar Fim Data Fito Takarar Gwamnar Kano-Karanta Kaji

Dandalin Kannywood: A Karon Farko Mace ‘Yar Fim Ta Fito Takarar Kujerar Gwamnar Kano

Jarumar kannywood Fati D,Isah wadda akafi sani da Fati D.Asirka ta fito takarar gwamnar kano a karkashin tutar jam’iyyar RP,ta kuma bayyana dalilinta na shiga siyasa da kuma kudirinta ga masana’antar kannywood dama jahar kano baki daya.

A hirarta da jaridar Daily trust Fati ta bayyana cewa sabon tsarin dokar kasa ta bawa matasa daar tsayawa takara,wanda hakan ya kara mata kaimi wajen tsayawa takara,bugu da kari kuma ganin kasancewar ana barin mata¬† a baya a al’amuran siyasa yasa taga dacewar tashiga a dama da ita.

A cewarta tana so ta canja tsarin siyasar kano da arewa yadda maza suka mamaye komai koda bata samu nasara ba a kalla ta kafa wani tarihi kuma ta zo da bakon abu kasancewa mace ta farko da tayi takarar gwamna a kano.

Har ila yau Fati ta fadi irin gwagwarmayar data sha kafin ta sami tiket din takara da yadda akayi primary election kuma aka zabe ta,wanda yanzu haka an damka mata tutar takara wanda dalilin haka ya bata damar kasancewa acikin ‘yan takarar da za’a gwabza dasu a zaben bana.

Fati ta bayyana irin gudunmuwar da take samu daga abokan sana’arta wajen bata shawarwari da kara tallata takararta wanda tace masana’antar kamar uwa daya suke dama wajen shiga lamuran juna na dadi ko akasin haka,ta kuma tabbatar da cewa in tayi nasara zata inganta harkar matuka wajen bawa masu kananan sana’o’i aciki irin masu kwalliya da haske tallafi da zasu inganta sana’arsu su kuma tsaya da kafar su.

Daga karshe ta zayyana kudurorinta ga jahar kano idan tasamu nasara zata tallafawa matasa zata bada ilimi kyauta a kowane mataki inganta fannin lafiya da ilimi,wuta da ruwa da sauran abubuwa na cigaba.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-02-03 — 9:34 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme