DALILIN DA YASA MUKA KARA KAMA SANATA DINO MALAYE — HUKUMAR YAN SANDA

DALILIN DA YASA MUKA SAKE KAMA SANATA DINO MALAYE — RUNDUNAR YAN SANDA

DAGA AUWAL M KURA
3/05/2018

#JARIDARTARAYYA

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana dalilan da Saya suka Sake Cafke Sanata Dino Melaye jim kadan bayan Kotu Ta bayar da belinsa kan Naira miliyan 90 a Babban Birnin Tarayya Abuja.

A ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan sanda suka gurfanar da Sanata Melaye da ke wakiltar Kogi ta Yamma a gaban kotun majistare da ke yankin Wuse Dake Abuja.
Kotun ta bayar da belinsa kan kudi Naira miliyan 90 amma kuma jim kadan da sakin sa sai ‘yan sandan suka sake cafke shi.
A sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce, sun sake kama Sanata Melaye saboda laifukan da ake zarginsa na hada baki wajen aikata mugganlaifuka da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Sanarwar da Kakakin Rundunar ‘Yan sandan najeriya Jimo Moshood ya sanya wa hannu ta ce, za su sake gurfanar da Melaye a gaban kotu ba tare da bata lokaci ba.
Kotun ta bayar da umarnin ‘yan sanda su ci gaba da tsare Sanatan har zaman shari’a na gaba.

This website uses cookies.