MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DALILAI 3 KA IYA HANA SHUGABA BUHARI TSAYAWA TAKARA A TENUWA TA 2 A ZABEN 2019

SHUGABA BUHARI BAZAI DAWO A TENUWA TA 2 BA SABODA DALILAI 3

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau karagar mulkin kasar a ranar Juma’a, 29 ga watan Mayun 2015, tun lokaci shugaba Buhari ya koma mulki, akwai abubuwa daban daban da yan Najeriya suna fuskanta musamman tabarbarewar tattalin arzikin kasa A jiya, Juma’a, 5 ga watan Mayu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya musanta rade raden da bashi da lafiya zai fito a gaban jama’a.

Shugaban Najeriya na yi sallar Juma’a tare da manyan-manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya a wani masallaci dake fadar shugaban kasa a babban birnin tarayyar Abuja. Meyesa wasu mutanen Najeriya suna fadin Shugaba Buhari ba zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2019 ba? Ku duba abubuwa 3 zasu yiwu hana dawowar mijin Aisha Muhammadu Buhari a 2019.
1. Rashin isasshen lafiyar jiki A watan Disamban 2016, Shugaba Buhari ya bar kasa nan na garin Landan dake kasar Ingila don rashin lafiya. Kafin ya tafi, wani mai magana da yawun shugaban kasa yace Ogansa na bukatar makonni 2 kawai na hutunsa. Amma, Shugaban Najeriya ya ci fiye da wata daya a kasar Ingila. Shugaba Buhari ba zai dawo a shekarar 2019 na tenuwa 2 ba saboda wadannan dalilai 3 Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnan jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun Idan ba zaku manta ba, shugaban kasa ya kasa halarci a ganawar majalisar zatarwa na sau uku kafin ya fito a jiya na Sallar Juma’a. Saboda haka, zai amfana da shan kwanta bayan 2019. Kuma, idan mutum yana da lafiyar jiki, yana da duk abu.
2. Shawarar yawan yan Najeriya Wasu mutanen Najeriya basu farin ciki da Shugaba Buhari. Menene dalilinsu? Dalilinsu yana kan rashin aiki, matsin tattalin arzikin kasa da matsaloli dabam dabam suna fukanta tun 2015. Don haka, basu so dawowar shi na tenuwa biyu a zabe mai zuwa.
3. Shugaban ya zama dattijo da ya bukatar shan kwanta Akwai wasu dattijai suna da karfi zasu manajin wahalar matsayin shugaban kasa. Amma, matsalar mukamin shugaban Najeriya na da yawa. Kuma, idan Shugaba Buhari bai yi hattara ba, zai cigaba rasa naman jikinshi sosai bisa gyaran matsalolin kasa nan.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-05-06 — 1:40 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme