MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DA SAURAN AIKI: Hukumar INEC Ta Lissafa Garuruwa 3 Da Za’a Sake Zaben Shugaban Kasa-Karanta kaji Dalili

Bata kare ba: Duk da Buhari ya lashe zabe, za’a sake zaben shugaban kasa a jihohi uku – Inji INEC .

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wto INEC ta bayyana cewa ta zabi ranar 9 ga watan Maris matsayin ranar sake gudanar da zaben shugaban kasa a wasu wuraren da aka samu matsala a ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

Kwamishanan labarai na hukumar INEC, Festus Okoye, ya bayyana cewa za’a gudanar da zaben ne tare da zaben gwamnoni da majalisar dokokin tarayya. Okoye ya ce an yanke wannan shawara ne bayan ganawar hukumar da wakilan INEC dake jihohin tarayya a ranar Alhamis, 28 ga watan Febrairu, 2019.

INEC ta yi watsi da zaben wasu wurare sakamakon rikice-rikice wanda ya hana hukumar aika kayan zabe da ma’aikata wajen domin kare rayukansu.

Wadannan wurare sun kunshi kananan hukumomi biyu a jihar Ribas, jihar Legas da jihar Anambara.

Jawabin yace: “Saboda haka, hukumar ta yanke shawara cewa za’a gudanar da zaben a dukkan wuraren da ba’a samu daman gudanar da zabe ba a ranan Asabar, 9 ga watan Maris tare da zaben gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha,”.

Za ku tuna cewa rikice-rikice a unguwar Okota dake jihar Legas ya sanda INEC tayi watsi da sakamakon zaben wajen, kana kashe-kashe da aka yi a jihar RIbas inda akalla mutane 20 suka rasa rayukansu ranar zabe.

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (2590 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2019-03-01 — 5:39 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme