MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Da gaske an yi wa Kwankwasiyya tawaye  Kano?

Wasu da suka yi ikirarin magoya bayan Kwankwasiyya ne sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a daidai lokacin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar takararsa ta neman shugabancin kasar a Abuja.

Daruruwan matuka babuwa masu kafa uku ne da aka fi sani Adaidaita Sahu a Kano da ke ikirarin cewa mabiya akidarsa ta kwankwaisiyya ne su kai wannan sauyi zuwa bangaren Gandujiyya mai mulki.

Jami`an gwamnatin jihar Kano ne suka karbe su, a wajen wani biki na musamman da aka gudanar a Kano.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce, inda wasu kafofin watsa labaran Kano suka rawaita cewa wasu masu baburan Adaidaita Sahu din suka yi ikirarin sauya shekar, sun yi korafin cewa ba a biya su kudin da aka yi musu alkawari ba.

Wasunsu sun shaidawa wani gidan rdiyo mai zaman kansa cewa, an tare su ne kawai a hanya aka ce su su je taron za a biya su, amma kuma sun nemi wanda zai biya su sama ko kasa sun rasa.

Ana dai zargin cewa gwamnatin jihar Kano ce ta shirya bikin domin dauke hankalin jama`a daga bikin da tsohon gwamnan ya shirya a Abuja, amma ta musanta.

Amma kwamishinan watsa labaran jihar Kano, Mallam Muhammad Garba ya ce sam ba haka lamarin ya ke ba.

Ya ce mutanen ne suka shirya sauya shekar don radin kansu, amma ba wai gwmanati ce ta dauki nauyin su ba.

Shugaban jam`iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abas shi ne ya jagoranci bikin karbarsu, wadanda suka yi ikirarin cewa sun kai akalla mutum dubu biyar.

Shugaban `yan Adaidaita Sahun, Mallam Usama Haruna Dala ya ce rashin kyautatawa ne ya tilasta musu kaurace wa gidan kwankwasiyya.

Wannan sauya sheka da `yan Adaidaita Sahu suka yi dai ba karamin kamu ba ne a wajen jiga-jigan gwamnatin APC a jihar Kano, kamar yadda Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso kwamishinan raya karkara na jihar Kano ya bayyana, inda ya ce sun gama tatike kwankwasiyya saura jagoranta:

An dade da raba-gari tsakanin gwamna Ganduje da senata Rabiu Kwankwaso a jihar Kano, amma adawar ta kara tsami bayan ficewar Kwankwason daga APC zuwa jam`iyyar PDP.

Kuma mabiya Gandujiyya da dama na kallon wannan neman takarar shugabancin kasar da Kwankwason ke yi a matsayin cin fuska ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, duk kuwa da cewa kundin tsarin mulkin Najeriyar bai haramta masa yin haka ba.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme