MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

BUBUWA GOMA DA SHUGABAN KASA BUHARI YAYI MAGANA AKAI A  RANAR DIMOKURADIYYA

BUBUWA GOMA DA SHUGABAN KASA BUHARI YAYI MAGANA AKAI A RANAR DIMOKURADIYYA

#JaridarTarayya

1. Bayan gaisuwa ga ‘yan Nijeriya a yau ne muke bukin murnar dawowar dimokuradiyya na 19 kuma na uku a wannan gwamnatin. Ina matukar gode wa Allah da ya kawo mu wannan rana. A gaskiya wannan gwamnatin ta zo a daidai lokacin da ‘yan Najeriya suke bukutar canji, kuma mun yi alkawarin za mu kawo masu canji. Mun fuskanci kalubale manya guda uku; rashin tsaro, cin hanci da rashawa da kuma matsalar tattalin arziki.
2. A wannan rana ina son in tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa lallai gwamnati za ta cika masu alkawuran da ta yi masu.
3. Samar da tsaron al’umma shi ne aikin da wannan gwamnati ta sa a gaba, kafin mu zo wannan matsayi Boko Haram ta kama wasu kananan hukumomi tana iko da su a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.
4. A yau gwanati ta yi kokarin wajen murkushe ayyukan ta’addanci ta kuma sanya an sako ‘yan matan Chibok 106 da kuma 104 na Dapchi da sama da mutane 16,000 wadanda Boko Haram suka sace.
5. Mun kuma samar da kula na musamman a sansanin ‘yan gudun hijra.
6. Muna nan kuma muna kokarin samar da wani shiri na musamman a kan masu garkuwa da mutane. Wannan shirin namu zai fara ne tun daga matakin karamar hukuma zuwa jiha zuwa gwamnatin tarayya.
7. Zan kuma yi amfani da wannan dama in godewa rundunar hadin gwiwa na samar da tsaro daga Kasashen Nijer da Benin da Chadi da Kamaru da suke haduwa da namu wajen murkushe ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
8. Allal hakika wannan gwamnati tana jin radidi da zafin hasarar rayuka da dukiyoyi da ake yi. Ina son in sanar da ‘yan Najeriya Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta zakulo masu aikata wannan abu an kuma hukunta su kamar yadda doka ta tanadar.
9. Yanki Niger Delta ma ya ci moriyar wannan gwamnati wajen samar masa da ayyukan da suka inganta rayuwar al’ummar yankin.
10. Abu na biyu da wanna gwamnati ta sanya a gaba shi ne yaki da cin hanci da rashawa.
Allah Ya Albarkaci Najerya

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-29 — 5:41 pm

1 Comment

Add a Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme