MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

BATUN GOBARAR HUKUMAR ZABE : EL-RUFA’I ZAI MAKA WANI MAI AMFANI DA YANAR GIZO A KOTU

El-rufai Zai Kai Karar Wani Mai Anfani Da Yanar Gizo Kotu Saboda Ya Danganta shi Da Gobarar Da Yafaru a Yau
Muryan yanci

DAGA LABARUN SIYASA

A safiyar yau ne gobarar wuta ya barke a hedikwatar hukumar zaben jihar Kaduna (SIECOM). Wanda yake sokoto road a cikin birnin jahar. Wannan hukuma ita ke da alhakin gudanar da zaben kananan hukumomi 23 Wanda ake shirin yinsa ranar 12 ga watan gobe.
Bayan faruwar lamarinne wani mai suna Steven kefas ya rubuta a shafinsa na twitter @realkefason
Da dumi duminsa:
Offishin hukumar zabe Yakama da wuta. Idan zamu iya tunawa ranar 12-5-18 za ayi zabe, wannan wani alama ne Wanda yanuna gwamna el-rufai bayason ayi wannan zaben.
Mr Kefas ya bayyana kanshi a matsayin Dan gwagwarmaya kuma mai sharhi akan yau da kullum daga kudancin Kaduna, wannan maganar dayayi akan gobarar yasa gwamnan ya mayar masa da martani ta @el-rufai;
Gwamnan el-rufai yace ” Kefas wannan rashin mutuncin naka da bata suna yana bukatar tankawa. Ina fatan idan kasami takardan sammaci daga kotu zakazo da hujjojinka. Muna binciken addreshinka saboda bayananda zamu bada a kotu kataimaka ma hanyar da zamubi wurin turo mana adireshinka. Kataimaka mana wajen ruromana da wuri.
El- rufai yacigaba da fada ma Kefas cewa
Mafi yawancin mutane suna ganin yanar gizo tabasu damar yin duk abinda sukeson yin batare da jin tsoron abinda zai biyo baya ba. Sufadi abinda suka ga dama, suyi kalaman batanci,su bata suna da cin mutuncin mutane. Akwai ka’idojin shari’a kuma ba wahalar ganuwa zakayi ba kamar yanda kake tunani.
Idan zamu iya tunawa gwamnan kwanan nan yakai karar shehu sani kara a high court inda yanima kotu tabashi naira billiyan biyu akan zargi hudu Wanda ciki har da zargin bata mai suna.
Lokaci ne kadai zai nuna mana ko gwamnan zai kai karan kamar yanda yai kudiri ko kuma shi Kefas din zai janye kalamansa kuma yanimi afuwa.
Haryanzu dai babu takamaiman dalilin aukuwar wannan gobarar har lokacinda muke rubuta wannan ruhoton

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-04-22 — 11:52 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme