MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Ba da Umurnin Janye ‘Yansandan dake Kare Wasu Ba Kan Ka’ida Ba

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Ba da Umurnin Janye ‘Yansandan dake Kare Wasu Ba Kan Ka’ida Ba

Yayinda ya gana da duk kwamishanonin ‘yan sandan Najeriya, babban sufeton ‘yan sandan kasar ya basu umurnin su janye duk wani jami’insu dake kare wani ba akan ka’ida ba nan da karshen wannan watan.
Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ba kwamishanonin ‘yan sandan kasar umurnin su janye duk wani dan sanda dake kare wani babban mutum ba kan ka’ida ba.
Babban sufeton yace dole ne su yi hakan kafin karshen wannan watan domin tabbatar da cikakken iko kan duk ‘yan sandan kasar.
Da yake bayyana ra’ayinsa akan wannan al’amari, Malam Sha’aibu Mungadi, wani mai sharhi, ya ce ba daidai bane a rinka ganin ‘yan sanda rike da jakunan matan sanatoci a kasuwa idan sun je sayen kaya ko yin cefane. Mungadi yace ko a gonakin manyan mutane ana kai ‘yan sanda suna tsaro yayinda ake barin talakawa zaune, ba tsaro. Ya ce ya taba ganin wani dan sanda da ya share shekaru goma yana aiki a gidan gwamna ba’a taba canza shi ba.

Koya Kuke Kallon Wannan Mataki Na Sufeto Janar Na yan Sandan Najeriya?

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-10-26 — 10:09 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme