MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Ba ni da ra’ayin siyasa ko kadan, ni fim ne sana’ata ba siyasa ba – Ali Nuhu

Ba ni da ra’ayin siyasa ko kadan, ni fim ne sana’ata ba siyasa ba in ji Jarumi Ali Nuhu

Shahararren Jarumin Kannywood ya bayyanawa BBC hausa Sashen Turanci cewa bazai taba shiga siyasa ba ko tsayawa takara.

An tambaya Ali Nuhu ko zai iya shiga fina-finan kasar Amurka na Hollywood a nan gaba kamar yadda yake yin na Kudancin Nijeriya?

Ali Nuhu ya bayyana cewa shi duk fim din da aka taya masa in dai har yana jin harshen da za a yi fim din to zai amsa tayin.

Ya kuma bayyana cewa; Ga masu cewa ba sa ganina a baya-bayan nan a fina-finan Kudancin Nijeriya, to sai dai idan ba sa kallon sabbin fina-finai ne don ba a dade ba ma na yi wani fim mai suna “Banana Island.”

An kuma tambayi Ali Nuhu koyana samun isasshen lokacin da yake kula da iyalinsa ganin cewar sana’ar tasu mai cin lokaci ce?

Sai ya ce “Kwarai ina samun lokacin da nake zama da iyalina da kuma kula da su sosai, musamman a wannan lokaci na azumin watan Ramadan, tun da ba mu faye dadewa a wajen al’amuran daukar fim ba.”

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-30 — 4:49 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme