Anyi Jana’izar mutane sama da talatin da wasu ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Birani dake karamar hukumar mulki ta Zurmi a jahar Zamfara

Copied from muawiyya abubakar zurmi

Anyi Jana’izar mutane sama da talatin da wasu ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Birani dake karamar hukumar mulki ta Zurmi a jahar Zamfara
.
Da yamancin jiya ne wasu yan bindiga suka kai mummunan hari a kauyen Birani dake cikin karamar hukumar mulki ta Zurmi dake Jahar Zamfara, ‘yan bindigar sun bude ma motar ‘yan kasuwa wuta motar tana dauke da mutanen kauyukan birani, tungar fulani, mayasa da mashema, daga bisani kuma suka cinna ma motar wuta wadda take dauke da dimbin mutane inda hakan yayi sanadiyar hasarar rayuka da jikkita mutane da dama.
Sudai ‘yan bindigar sun tare wata hanya ne dake fita garin na Birani sukayi masu kwanton bauna inda suka tare wata motar ‘yan kasuwa kirar (kanta). ‘yan kasuwar sun gama cin kasuwa ne kamar yanda suka saba duk sati a hanyarsu ta zuwa garuruwansu sai ‘yan bindigar suka bude ma motar wuta tare da kone dukkan mutanen dake ciki kuma suka cigaba da kashe mutane da sunkayi yunkurin kawo masu dauki.


Daga cikin muhimman mutanen da suka samu halartar sallar jana’izar akwai maimartaba sarkin Zamfaran Zurmi Alhaji Abubakar Atiku Muhammad, shugaban karamar hukumar mulki ta Zurmi Hon Dr Auwal Bawa Moriki, Hon Mannir Aliyu gidan Jaja, Hon Yusuf Moriki dadai sauran mutane da dama

This website uses cookies.