MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ANA WATA GA WATA: AN DAKATAR DA HAKIMAI BIYU DA SUKA SHIRYA TARON YIWA BUHARI ADDU’A A GOMBE

Abin Takaici: An Dakatar Da Wasu Hakimai Biyu A Gombe Akan Shiryawa Buhari Taron Addu’a

Masu Rahotanni sun kawo cewa mai martaba sarkin Deba ya dakatar da wasu Hakimai biyu da ke karkashin masarautar sa sakamakon gudanar da taron yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’o’i a garuruwan su da suka yi. Hakiman da aka dakatar sune, hakimin Garin Mallam Alhaji Julde da Ummaru Bappayo na garin Wajari.

A wasikar da sakataren masarautar Deba, Saidu Mele ya mika wa Hakiman, ba a bayyana dalilin da ya sa aka dakatar da su ba amma an ce daga wannan rana su kwabe rawaninsu su har sai sun ji daga masarautar.

An dakatar da Hakimai 2 saboda shirya taron yi wa Buhari addu’o’i a jihar Gombe “Daga yau an dakatar da ku daga ci gaba da sarautar garuruwan ku.” Julde ya bayyana wa majiyarmu ta Premium Times cewa yana da yakinin cewa gwamnatin jihar ne ta sa ayi musu haka. KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta aika sammaci ga jakadan Amurka Ita ko masarautar Deba karyata wannan korafi da hakiman suka yi tayi inda ta ce babu sarkin da ya dakatar da wani hakimi saboda wai ya shirya taron yi wa Buhari addu’o’i, su dai su bayyana laifukan su na gaskiya.

Shima Kwamishinan Yada Labarai na jihar Umar Nafada, ya bayyana cewa bashi da masaniya game da wannan zance na dakatar da wasu hakimai don sun yi wa Buhari addu’o’i.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-12-04 — 3:02 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme