AN WARE DALA BILYAN 34.7 DIMIN GINA GURAREN SHAKATAWA A SAUDIYA

TIRKASHI:

AN WARE DALA BILYAN 34.7 DOMIN GINA GIDAJEN SHAKATAWA A SAUDIYA

#JaridarTarayya

Kasar Saudiyya ta zuba zunzurutun kudi,dalar Amurka biliyan 34,7 don gina wuraren shakatawa,na kashe kwarkwatan idanu,raye-raye da na kide-kide.
Shugabannin Saudiyyan sun yanke wannan shawarar da nufin maida kasarsu cibiyar raya al’adu da ta shakatawa wacce babu kamar ta a duk fadin yankin gabas ta tsakiya.
A ranar Alhamis din nan da ta gabata,hukumomin Saudiyya sun zuba dalar Amurka biliyan 130 don sayen fina-finan da nuna a kasarsu har ya zuwa shekarar 2020.
Shugaban lamurran da suka danganci al’adu a kasar ta Saudiyya,Ahmad al-Mazid ya ce,
“Manufarmu ita ce zama gagara gasa a fannin fina-finai,sinima da raya al’adu”
A sahun aiyukan da za a kaddamar a yanzu haka,akwai gina wuraren shakatawa 16,wurin waha daya da kuma manya-manyan cibiyoyin saye da sayarwa 3.
Za gudanar da dukannin gine-gine da zummar sanya sunayen biraren Saudiyya,a jerin sunayen biranen duniya mafiya kyau da dadin rayuwa.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya,Muhammad bin Salman ne ke jan ragamar wadannan sauye-sayen.

This website uses cookies.