AN KUSA SACE ATIKU A JAHAR TARABAR

TIRKASHI

AN KUSA SACE ATIKU A JAHAR TARABA

Daga Auwal M Kura
1/04/218

Rundunar Yan Sandan Jahar Taraba a Ranar Juma’a 30/03/2018 Tayi Nasarar Kubutar Da Wani Mutum Mai Suna Alhaji Atiku Yakubu ,Bayan Wasu Yan Ta’adda Sunyi Yunkurin Saceshi A Gidansa Dake Garba-Chede A Karamar Hukumar Gossol Dake Jahar Ta Tararaba ,Inda Jami’an Yan Sandan Sukayi Nasarar Harbe Biyar Daga Cikinsu

ASP David Misal, Shine Mai Magana Da Yawun Rundunar Yan Sanda Ta Jahar Taraba, Ya Tabbatar Da Faruwar Lamarin Yayi Dayake Zantawa Da Manema Labarai A Ranar Asabar Din Nan Data Gabata a Babbban Birnin Jahar Jalingo.
Misal Yace”Jami’anmu Dake Bali Dibishan A Ranar 30/03/2018 Da Misalin Sha Daya Na Dare Suka Samu Masaniayr Cewa Wasu Gungun Gun Barayi Da Garkuwa Da Mutane Sun Zagaye Gidan Alhaji Atiku Yakubu Dake Garba-Chede Domin Suyi Garkuwa Dashi, Inda Nan Take Hazikan Jami’an Mu Suka Bayyana Gurin Inda Akayi Batakshi Da Harbe Harbe ,Kuma Jami’an Namu Sukayi Nasarar Kashe Mutum Biyar Da Kwace Wasu Makamai Daga Hannun Yan Ta’addan ”

A Karshe Asp Misal. Yayi Kira Ga Al-ummar Jahar Dasu Kwantar Da Hankalinsu Sannan Da Sunga Wani Abunda Basu Yarda Dashi Suyi Maza Sunarda Jami’an Yan Sanda Dake Kusa Ko Wasu Jami’an Tsaro Rahoto Domin Daukar Mataki

This website uses cookies.