MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

An kama barauniyar da ke yi wa ‘yan acaba tayin alawa, da sun sha sai su mika mata makulli

A yau Alhamis ne rundunar ‘yan

sandan jihar Katsina ta kama wata
barauniya mai suna Zinatu Abubakar da laifin sace babur.

Jami’in hulda da jama’a na
rundunar Gambo Isa ya sanar da
haka wa manema labarai a garin
Katsina.

Ya ce Zinatu ta hau babur din wani
mutum mai suna Gide Wada cewa
zai kai ta rukunin gidajen unguwar
Rima dake cikin garin Katsina daga
Kofar Kaura inda ta tsayar da shi.

” Sai Zinat ta yi wa Wada tayin
alewar chakulat yayin da suka fara
tafiya ai ko bayan ya gama tsotsan
wannan alewar sai ya fara ganin jiri.

” Sanadiyyar haka sai Wada ya
tsayar da babur amma kafin ya
ankare wasu abokan Zinatu masu
suna Abubakar da Chairman suka
diran masa inda suka yi korarin
kwace babur din da karfin tsiya. Da
Wada ya ga bazai iya da su ba sai ya
kwantsama ihu nan-nan ko mutane
suka kawo masa agaji.

Isa ya ce mutanen sun cafke Zinatu
sannan Abubakar da Chairman suka
tsere.

Ya ce bincike ya tabbatar musu
cewa Zinatu da abokanta na cikin
wata kungiyar ‘yan bata gari dake
sace wa ‘yan achaba babura kuma
an gano sun dade suna aikata
wannan ta’asa a Kaduna da Kano.

A karshe Isa ya yi kira ga duk ‘yan
achaba da su guji karban abinci daga hannun mutanen da basu san su ba.

Ya ce rundunar ta fara farautan
Abubakar da Chairman don gurfanar
da su.

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (1488 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-08-31 — 8:53 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme