MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

AN HARBE YAN SANDA TARE DA SACE MUTANE SHA BAKWAI CIKI HAR DA AMARE BIYU A JAHAR KADUNA

YAN BINDIGA A SUN KASHE YAN SANDA TARE DA SACE MUTANE SHA BAKWAI CIKI HAR DA AMARE BIYU A JAHAR KADUNA
Daga Auwal M Kura
13/04/2018

A kalla Jami’an Yan Sanda Biyu Da Dan Yuniyan Daya Yan Bindiga Suka Harbe Har Lahira A Garin Ciki Da Falo Dake Karamar Hukumar Birnin Gwari Ta Jahar Kaduna ,

Lamarin Yafaru ne Jiya Al-hamis 12/04/2018 Kamar Yadda Rohotonin Suka Tabbatar Yan Bindigan Kuma Sunyi Awon Gaba Da Mutane Sha Biyu Da Kuma Amare Biyu Inda Sukayi Garkuwa Dasu ,

Austin Iwar, Shine Kwamishina. Yan Sanda Na Jahar Kaduna, Wanda Ya Tabbatar Da Faruwar Lamarin,inda Ya Kara Da Cewa A Satin Daya Gabata Ma Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Mutum Biyar Ciki har da Sarkin Kauyen Garin Dan Sarari Dake Karamar Hukumar Birnin Gwari .

A Nashi Bangaren Sarkin Birnin Gwari Zubairu Mai Gwari, Ya Sake Kira Ga Al-ummar Yankin Dasu Tsaya Domin Kare Kansu, Inda Ya Kara Da Cewa” Babu Yadda Za’ayi Mutsaya Muna Jiran Wani Wanda Bazai Zo Ba Muce Ya Karemu. muba Wawaye Bane Kuma Babu Wanda Ya’isa Ya Hanani Fadawa Al-ummata Su Kare Kansu Daga Yan Ta’adda. Domin Kuwa Babu Wadatattun Jami’an Tsaro Da Zasu Iyya Karesu” – Inji Sarkin Birnin Gwari.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-04-13 — 6:33 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme