MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

allah ya rabamu da bakin hali, DUBA ABUN DA WANI YAYIMA DAN MATARSA

An zargi wani mutumin Najeriya da cin zarafin dan matarsa mai shekaru 6 saboda bai siyo masa abun da ya aike sa ba. An tattaro cewa mutumin da ba’a ambaci sunan sa ba ya yi ma dan matarsa mugun duka saboda yaron ya yi kuskure gurin siyo abun da aka aike shi. An aiki yaron wanda aka kira da Emmanuel ya siyo wa mijin mahaifiyarsa sigari sai ya manta ya siyo biredi a maimakon haka. NAIJ.com ta ci karo da labarin yaron ne bayan a yada a wani shafin Instagram mai suna Basic Rights Counsel (BRC). A cewar hukumar Basic Rights Counsel, bayan sun ji labarin Emmanuel, sun aika tawagar ceto zuwa gidan yaron.A take aka kai yaron wani babban asibiti amman da suka isa asibitin sai aka gano cewa gwiwar hannunsa ta samu matsala. An mayar da Emmanuel asibitin koyarwa don samun cikakken kulawa. Allah ya kyauta don kawai yayi kuskure.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-05-27 — 2:01 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme