MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Alhazan Najeriya uku sun rasu a hadarin mota a kusa da Madina

Shugaban kula da lafiyar Alhazai na
hukumar NAHCON Ibrahim Kana ya
tabbatar wa manema labarai cewa
wasu alhazai daga jihar Zamfara sun rasu a hadarin mota daga Madina zuwa Makka a safiyar Juma’a.

Alhazan da suka rasu sun hada da
Shinkafi Mudi Mallamawa, Abdullahi
Jafaru Gidan Sambo,da Abdullahi
Shugaba.

An aika da gawarwakin wadannan
Alhazai da suka rasu asibitin Sarki
Fahad dake Madina, inda sauran
wadanda suka ji ciwo aka kwantar
dasu a wani asibiti dake kusa da
Madinna.

Shugaban kungiyar ‘yan jarida na
jihar Zamfara Abdulrazak Kaura da
shi ma yanzu haka yana kasar Saudi
ya ce dukkan wadanda suka rasu
shugabannin jam’iyyar APC ne a
kananan hukumomin Zamfara.

” Jafarau Gidan Sambo shine
shugaban APC na karamar hukumar
Kaura Namoda, Mudi Mallamawa na
Shinkafi sannan Abdullahi Shugaba
na Karamar hukumar Maru.”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-09-01 — 7:18 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme