MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Akwai Yiyuwar Hukumar Yan Sanda zata kama shugaban Majalisar Dattawa Wato Bukola Saraki

Akwai Yiyuwar Hukumar Yan Sanda zata kama shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Wata majiyar jaridar ” Premium Times” ya nuna cewa Shugaba Muhammad Buhari ya amincewa Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda, Ibrahim Idiris kan ya cafke Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki bisa zarginsa dahannun kan kisan akalla mutane 20 a wani Fashin banki da aka yi a garin Offa da ke jihar Kwara.

Majiyar ta nuna cewa a ranar Juma’a ne Shugaban ‘yan sandan ya ziyarci Buhari a fadarsa inda ya yi masa bayani game da tuhumar da ‘yan sanda ke yiwa Saraki wanda shi kuma Buhari ya nuna cewa babu wanda ya fi karfin doka a kasa.

Tun da farko dai rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa ta kama mutane biyar daga cikin ‘yan fashin kuma sun yi ikirarin cewa Saraki da kuma Gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed suka dauki nauyinsu. An yi amfani da motar Madugun ‘yan fashin mai suna Ayoade Akinnibosun, mai shekaru 37, ne wanda kuma a lambar motar akwai sunan Saraki.

KARANTA KAJI: WASU DA AKE ZARGI DA LAIFIN KISA SUN BAYYANA CEWA SARAKI NE KE DAUKAR NAUYIN SU

Daga cikin jami’an gwamnatin Kwara da ake zargi da hannu a fashin Bankin har da Shugaban ma’aikatan Fadar gwamnatin jihar Kwara, Yusuf Abdulwahab. Tuni dai rundunar ‘yan sanda ta gayyato Shugaban majalisar Dattawan don yin bayani game da zargin da ake yi masa.

Da yake musanta zargin, Saraki ya nuna cewa Shugaban ‘yan sandan ya kulla masa wannan makircin ne son kawai ya kunyata shi a idon duniya inda ya nemi al’ummar Nijeriya su yi watsi da wannan zargin sannan ya bayar da tabbacin cewa zai gaggauta mika kansa ga ‘yan sanda don amsa gayyatar rundunar.

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-06-04 — 10:35 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme