MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ABIN MAMAKI: KU KALLI BIDIYON SANATA DINO MELAYE YANA TALLAR GYADA AKAN TITI-Duba Kaga

                 Bidiyon Sanata Dino Melaye ya na saida gyada a kai ya jawo magana

Mun samu labari cewa wani bidiyo da aka ga ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Yankin Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawa watau Dino Melaye ya na saida gyada a kan sa ya ba jama’a mamaki.

Sanata Dino Melaye lokacin da yake tallar gyada An hangi Sanata Dino Melaye wanda ba bakon jawo magana bane yana tallar dafaffiyar gyada daure a saman kan sa. Wasu sun yi wuf sun dauki Senata Melaye hoto lokacin da yake wannan talla a kan titi dauke da kwano.

Ana tunani wannan abu ya faru ne tun a bara, sai dai yanzu ne hankalin mutane ya karkata zuwa bidiyon. ‘Dan Majalisar ya kuwa yi ciniki inda jama’a da dama su ka tsaya su ka saye gyadar domin katse yawun marmari.

Wata Baiwar Allah ta nemi Sanatan ya rage mata farashin gyadar inda ya nuna cewa fau-fau ba zai yi rangwame ba domin farashin kaya sun tashi a zamanin Shugaba Buhari. ‘Dan Majalisar yana cikin ‘Yan adawar Gwamnatin nan. An ji Sanata Melaye yana cewa ba zai saida gwagwani 3 na gyadan a Naira 100 ba.

‘Dan Majalisar yace yana saida kowane gwangwani a kan kudi Naira 50 har yayi ‘yar shagube ga Shugaba Buhari mai kokarin yaki da barna a kasar. Kun san cewa Sanata Ben Bruce ya bayyana shirin da APC ta ke yi a Majalisa.

Ben Murray Bruce ya kuma bayyana cewa su na magana da kasashen waje domin ganin Gwamnatin Shugaba Buhari ba ta yi wa Majalisa katsalandan ba.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-09 — 12:59 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme