MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ABIN AL’AJABI: AN YANKEWA WANI MUTUM HUKUNCIN DAUREN RAI DA RAI SABODA YAYI TUSA A MASALLACI

An yankewa wani hukuncin rai-da-rai kan yawaita tusa a masallaci.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa wani alkalin Kasar Pakistan ya yanke ma wani matashi mai suna Mohammed Al-Wahabi mai shekaru 33 a duniya hukuncin daurin rai-da-rai,an yanke wa matashin hukuncin ne sakamakon yawan tusa da ya yi har sau 17 a masallatai guda shidda cikin watan Ramadan.

A cewar rahoton, alkalin ya bayyana cewa yawan tusan da dinga yi ya yi sanadiyan da mutane 53 suka bar masallaci a take, a lokacin da ake sahun salla ga mutane da suka halarci masallacin domin yin ibada a wata mai tsarki, don haka ne aka hukuntashi kamar yadda shari’a ta tanadar. An yankewa wani hukuncin rai-da-rai kan yawaita tusa a masallaci

Alkalin kotun ya ba matashin zabi a tsakanin, dauri, yanke masa kai ko kuma jifa. Mai laifin ya bayyana cewa yana fama ne da matsanancin cutar tusa, amma babu wani alkali day a tsaya masa.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-07-07 — 2:35 pm

1 Comment

Add a Comment
  1. Wata shariar ai sai a lahira Allah ne masani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme