MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

A KARSHE DAI ANYI NASARAR KAMA SANATA DINO MALAYE

A KARSHE DAI ANYI NASARAR CAFKE SANATA DINO MALAYE

DAGA AUWAL M KURA

23/04/2018

Rundunar Yan Sandan Najeriya Tayi Nasarar Kama Sanata Dino Malaye A Sanyi Safiyar Yau 23/04/2018 A Abuja.

Shugaban Kwamitin Kula Da Birnin Tarayya Na Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Dino Malaye An Ruwaito Cewa Ya Shiga Hannu Ne Jim kadan Bayan Isar Sa Filin Jirgin Sama Na Kasa Da Kasa Wato Nnamdi Azikiwe International Airport,Dake Birnin Tarayya Abuja.

Kamar Yadda Majiyarmu Ta Daily Trust Ta Haikaito, Cewa” Yayin Da Ake Tattaunawa Da Sanata Dino Malaye Kan Lamarin,Yace ” Na Isa Filin Jirgi Domin Tafiya Wani Muhimmin Al-amari Wanda Gwamnatin Tarayya Ta Turani , Amma Koda Na Iso Sai Akace An Bukatar Hankali A Offishin Hukumar Shiga Da Fita Ta Kasa,Koda Na Isa Sai Sukace Sun Kamani Bisa Umarnin Rundunar Yan Sanda Ta Kasa” -inji Malaye.

Har Yanzu Da Sanata Dino Malaye Yana Tsare A Hannun Hukumar Shiga da Fita Ta Kasa Kafin Mikashi Hannun Hukumar Yan Sanda

Idan Zaku Iyya Tunawa A Watan Daya Gabata ne Rundunar Yan Sanda Najeriya Ta Ayyana Sanata Dino Malaye Ruwa A Jallo, Bisa Zarginsa Da Daukar Nauyin Wasu Yan Ta’adda.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-04-23 — 9:43 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme