MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

A HARBE DUK WANI DAN TA’ADDA DA’A KAMA DAUKE DA BINDIGA — GWAMNAN ZAMFARA

A HARBE DUK WANI DAN TA’ADDA DA AKA KAMA DA BINDIGA – GWAMNAN JAHAR ZAMFARA

Daga Auwal M Kura

Gwamnan Jahar Dr Abdul’aziz Yari Yabada Umarnin Harbe Duk wani Dan Ta’adda Ko Duk Wani Da’aka Ga bindiga A Wuyanshi Yana Yawo Da Ita Da Aka Kama A Fadin Jahar Nan Take.

Da Yake Tattaunawa Da Manema Labarai A Gidansa Dake Talatar mafara Gwamnan Yace “A Halin Yanzu Mun Samu Rahoton Mutuwar Mutane 34 Dalilin Harin Da Yan Ta’addar A Karamar Hukumar Anka Dake Jahar,”

Gwamnan Ya Kara Da Jadda Duk Wani Dan Ta’adda Ko Mai Garkuwa Da Mutane Da’aka Kama A Jahar A harbe shi Nan Take Batare Da Wata Wata Ba ,

A Karshe Gwamna Abdul’aziz Yari Ya Ja Kunnen Masu Bawa Yan Ta’addan Mafaka Ko Wa’yan Da Ake Aikowa Amsar Kudin Fansa Cewa Duk Wani Da’aka Kama Hukuncin Daya Dana Yan Ta’addar Wato Kisa

Ko Kuna Ganin Wannan Hukunci Da Gwamnan Ya Yanke Yayi Daidai

Updated: 2018-03-30 — 8:35 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme