MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

2019: Bukola Saraki zai yi takara da Buhari

A cewar jaridar ta Bloomberg, Saraki ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shi a gidansa dake Abuja: “Ina tuntuba kuma ina da karsashin yin takara. Na san cewar zan kawowa Najeriya canjin da take bukata,” a kalaman Saraki. A ‘yan kwanakin da suka wuce ne Saraki ya fita daga jam’iyyar APC tare da komawa PDP, jam’iyyar da a cikinta ya zama gwamna a jiharsa ta Kwara sannan kuma ya zama Sanata.

Ana alakanta fitar Saraki daga APC da niyyarsa ta son yin takarar shugaban kasa. Saraki ya shiga jerin su Atiku, Kwankwaso, Makarfi, Lamido, Tanimu Turaki, Dankwambo da Tambuwal, da suke burin yiwa PDP takarar shugaban kasa.

A ranar Litinin ne Saraki, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Obasanjo inda suka shafe kusan sa’o’i biyu suna tattaunawa. Saraki ya ziyarci Obasanjo ne a gidansa dake hade da dakin karatun da ya gina a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Saraki ya isa gidan na Obasanjo ne da misalign karfe 5:30 na yamma cikin bakar babbar mota kirar Toyota Land Cruiser tare da wasu jami’an tsaron sa kuma ya bar gidan da misalin karfe 7:12 na dare.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme