MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

YADDA ZAKA TSARE FACEBOOK DINKA DAGA MASU KUTSE

HANYA TA FARKO (1) DA SUKE AMFANI DA ITA WAJEN SATAR ACCOUNT DIN FACEBOOK

Daga Arewa Times

Hanya mafi sauki da masheka ke amfani da ita wajen satar kundin ka na facebook shine ta hanyar amfani da link wajen yin login.

ABINDA YA KAMATA KA SANI
www.facebook.com ko www.fb.com sune kadai ingantaccen adireshin da akeyin login a facebook dasu.

Ka kula da kyau akwai wasu links da zaka gani wanda (sub domain ne) misali www.facebook.com/kanawa.com duk sanda ka ga link an saka facebook.com sannan an kara wani site a gaba, to ko da wasa kada ka kuskura kayi login tanan kana shiga zai baka dama ka sanya email da password dinka shikenan tamkar ka turawa wani password dinka ne.

Daga nan ka basu dama su ci karensu babu babbaka, da akwai tarin irin wannan links din suna yawo ana yawan turawa mutum su ta #WhatsApp ace ka shiga kayi login, don haka ‘yan uwa sai a kula.

Zamu dakata a nan sai a rubutu na biyu

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (2392 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-04-21 — 10:38 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme