MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Shahararren masanin ilmin sararin sama Zhang Heng

Zhang Heng an haife shi ne a gundumar Nanyang ta lardin Henan a tsakiyar kasar Sin. Tun lokacin da ya ke yaro ne ya yi kokari a wajen karatu, kuma ya gwanance a wajen wallafe wallafe. A lokacin da ya ke da shekaru 17 da haifuwa ne ya bar garinsu ya je Changan, wato birnin da ya zama hedkwatar kasa na sarauta da dama a kan tarihin kasar Sin. A nan Zhang Heng ya yi bincike da nazarin abubuwan tarihi, ya bincike al’adun jama’a da tattalin arzikin zaman tarayya. Daga bisani gwamnati na wancan zamani ta nada shi ya zama jami’I na Luoyang, daga baya kuma ya kama sauran mukamai.

Zhang Heng ya yi sha’awar ilmin halitta kwarai da gaske, amma ba ya sha’awar suna da riba, ya yi murabus har sau biyu. Ya yi shekaru 3 yana bincike firosufiya da lissafi da ilmin sararin sama, ya samu ilmi da yawa, kuma ya fara wallafa littafi.

A zamanin sarautar Han wato kafin shekaru dubu 2, akwai hasashe da dama game da samaniya. A ganin Zhang Hen, duniya ta yi kama da kwai, kasar da mu ke zaune ta yi kama da rawayan kwai, samaniya ta fi kasa girma. Wannan ra’ayinsa yana da ci gaba kwarai a wancan zamani. A ganinsa tun can farko duniya a harhade ta ke, amma daga baya, abubuwa maras nauyi sun yi sama sun zama samaniya, abubuwa masu nauyi sun nutsa har sun zama kasa. A ganinsa nisan da ke tsakanin taurari ne ya kudura saurin tafiyar taurari.

Zhang Heng bai bincike hasashe kawai ba, kuma ya sa muhimmanci a wajen yin aikatawa. Shi kansa ne ya bincike da kera kayayyaki da yawa na auna sararin sama da kasa. Misali ya kago wata na’urar auna girgizar kasa. A shekara ta 138, wannan na’urar auna girgizar kasa ta yi nasarar auna girgizar kasa da aka yi a lardin Shanxi.

Zhang Heng kuma ya bincike ilmin sararin sama da yawa. Misali ya ce, a tsakiyar kasar Sin ana iya gani taurari misali dubu 2 da 500. A ganin zhang Heng, ko da ya ke da safe da yamma, in an duba rana, ta yi girma, amma da tsakar rana ta yi karama, amma hasali ma daya ne, domin da sassafe da magariba, duniya ta yi dan duhu. Amma da tsakar rana, da haske da yawa, shi ya sa an yi tsammani rana ta yi karama. Misali in an duba wuta da dare, ta kan yi girma, amma da rana ta kan yi karama. Irin wannan ra’ayin Zhang Heng yana da gaskiya.

Zhang Heng kuma ya bincike ilmin sararin sama da yawa. Misali ya ce, a tsakiyar kasar Sin ana iya gani taurari misali dubu 2 da 500. A ganin zhang Heng, ko da ya ke da safe da yamma, in an duba rana, ta yi girma, amma da tsakar rana ta yi karama, amma hasali ma daya ne, domin da sassafe da magariba, duniya ta yi dan duhu. Amma da tsakar rana, da haske da yawa, shi ya sa an yi tsammani rana ta yi karama. Misali in an duba wuta da dare, ta kan yi girma, amma da rana ta kan yi karama. Irin wannan ra’ayin Zhang Heng yana da gaskiya.

Zhang Heng ba masanin ilmin sararin sama kawai ba, kuma shahararren mawallafi ne na zamanin Donghan, kuma ya gwanance a wajen zane. Shi ne daya daga cikin shahararrun masu zane 6 na wancan zamani. Bisa lissafin da aka yi an ce, Zhang Heng ya wallafa littatafai har 32 don nuna ra’ayinsa game da ‘yan Adam da karatu. A cikin littatafan da ya wallafa kuma ya siffanta al’amura na wancan zamani wadanda su ke da daraja kwarai a wajen bincike tarihi na wancan zamani. (Dogonyaro)

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-02-18 — 10:45 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme