SHAHARARREN JARUMIN FINA FINAN INDIYA SALMAN KHAN YAZAMA SAHUN MASU KIRA WAYAR HANNU

Salman Khan Ya Shiga Sahun Masu Kera Wayoyin Hannu

Shahararran Jarumin Bollywood Salmam Khan zai fitar da wata sabuwar waya samfurin Android mai suna ‘Being Smart’.

Yanzu haka jarumin na kammala shirye shiryen kaddamar da wayar tare da hadin gwiwar ‘yar uwarsa Alvira Agnihotri.

Wayar wacce za a sayar a akan farashin dalar Amurka 300 an yi ta ne saboda masu matsakaitan karfi, kuma za a fara sayar da ita ta yanar gizo.

Wayar za ta kuma kara da wayoyin kasar Indiya kamar su Oneplus, Oppo da Micromax.

Salman Khan ya na da nufin zuba duk ribar da ya samu daga sayar da wayar a asusun kungiyoyin sa masu zaman kansu da ya kafa domin tallafawa jama’a.

This website uses cookies.