MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: HANYOYI 2 DA ZAKA IYA MAIDA MAHIMMAN SAKONNIN KA NA WHATSAPP DAGA TSOHUWAR WAYAR KA ZUWA SABUWA

MATAKAI 2 DA ZAKA IYA DAWO DA SAKONNIN KA NA WHATSAPP DAGA KAN TSOHUWAR WAYAR KA ZUWA SABUWA.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Lokuta da dama jama’a basu jindadin rasa wasu mahimman sakona dake ficewa daga wayoyin su,bayan sun canza wata waya sabuwa.

A dalilin haka yasa wanda keda hakkin mallakar whatsapp ya kirkiro wata sabuwar hanya a saukake,don ganin an magance matsalar.

Whatsapp dai wata hanya ce ta isar da sako a saukake zuwa ko wacce kasa ko gari, tsakanin abokai,ta hanyar amfani da lambobin juna mutum daya zuwa 2 ko fiye da haka  a zauren hira ko muhawara.

Har ila yau whatsapp yana  daya daga cikin zauren hira daya samu daukaka da karbuwa a tsakanin al’umma da dama a duniya,wanda kusan ko wacce kusarwa ana amfani dashi tundaga kan:>’Yan kasuwa,’Yan makaranta,Office,Saurayi da budurwa da dai sauran su.

A bisa bincike da nazari da Dandalin mujallarmu,tayi ta kawo muku wasu hanyoyi a fayyace da zaku iya tsirartar da sakononin tsofaffin wayoyin ku zuwa sabbi da kuka canza.

Ga Yadda Zakayi Amfani Da Hanyoyin A Saukake Kamar Haka :-

MATAN FARKO ZAKAYI AMFANI DASU NE KADAI IDAN KANA AMFANI DA MEMORY , BA KAN MEMORY NA KWAKWALWAR WAYAR BA,YA RABU KASHI  4.

1- Zaka bude tsohon whatsapp dake acikin tsohuwar wayarka,sannan sai ka tafi zuwa (SETTING),bayan ka shiga setting din zaka zabi (CHATS AND CALLS) daga nan saika danna (BACK UP CHATS).

2- Wannan mataki zaiyi amfani ne kadai akan (BACKUP) inda daga nan sai ka koma baya wato (SETTING MENU),amma ba whatsapp Setting ba, (PHONE SETTING) ake nufi) sai ka shiga (EJECT SD CARD OPTION),ma’ana inda zaka cire memory card din daga kan waya batare da ka kashe wayar ba.

3- mataki na 3 shi zaka sanya sabon whatsapp akan sabuwar wayarka,sannan sai ka sanya memory din daka cire daga tsohuwar wayar ka, ka sanya shi acikin sabuwar.

4- Wannan mataki shine na karshe a tsarin amfani da memory a waya, bayan ka sanya memory din akan sabuwar wayar daga nan sai ka bude whatsapp din ka,kasa lambar da kake amfani da ita a waccan tsohuwar wayar.

Bayan ka sanya lambar zaka dan jira zuwa kamar minti daya kafin ya gama processin,idan ya gama zai nuna alama kamar haka (RESTORE) daga nan sai ka danna shi, toh ina tabbata maka daga wannan lokacin duk wani sakonninka dake a waccan tsohuwar wayar na whatsapp duk zasu soma dawo wa akan wannan sabuwar wayar taka.

MATAKAI NA BIYU ZAKAYI AMFANI DASU NE KADAI IDAN WAYARKA BAKA AMFANI DA MEMORY SAI DAI KWALKWALWAR WAYA,SU KUMA SUN RABU KASHI 6

1- Zakayi (BACK-UP) na dukkanin sakonnin ka dake a whatsapp a tsohuwar wayar ka,ta hanyar amfani da (GOOGLE-DRIVE).

2- Zaka sanya sabon whatsapp a wayar ka,kamar yadda yazo a waccan tsarin na baya.

3- Wannan mataki din ba’a bukatar ka fara sanya lambar da sunan bude sabon whatsapp din,har sai kayi (LOG-IN) na (GOOGLE-ACCOUNT) naka akan sabuwar wayar ka.

Amma kayi amfani da google acoount din kamar yadda kayi amfani dashi a tsohuwar wayar ka.

4- Yi amfani da lamba ire daya da wadda kayi amfani da ita a tsohon whatsapp din ka dake a waccan,tsohuwar wayar.

Bayan ka sanya lambar zaka dan jira zuwa minti daya,idan ya gama (PROCESSING) zai nuna maka zabi a rubuce kamar haka (OPTION TO RESTORE) kai kuma sai ka zabi (GOOGLE-DRIVE) inda anan goole account naka yake,domin ka dawo da mahimman sakonninka amma ka tabbata ka zabi google account din da kayi log in acikin sabuwar waya din.

5- Bayan (RESTORE ) din ya gama zaka danna (NEXT) daga nan duk wasu sakonninka zasu fara dawowa duka,jim kadan zuwa lokaci kalilan.

6- Wannan shine mataki na karshe a tsarin da idan mutum na amfani da kwakwalwar waya,ba memory card ba.

Bayan kammala dawo maka da sakonninka da abokanka suka turo maka a waccan tsohuwar wayar sun nuna akan wannan sabon whatsapp din da ka bude a sabuwar wayar ka,toh daga nan sai wakokin da bidiyo da voice note da hotuna  zasu fara dawo wa.

Bayan komi ya tsaya cak,shikenan aikin ka ya kammala,daga nan zaka iya goge abubuwan dake kan tsohuwar wayar ka idan kaso ma’anna kayi (RESTORE FACTORY).

Ku Kasance Da Dandalin Mujallarmu Akoda Yaushe Domin Amfana Da abubuwa Na Cigaba.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-09-18 — 7:01 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme