MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Hanyoyi 6 da waya ke cutar da rayuwar dan Adam Musamman Na 3 da na 4

Tabbas Waya ta kawo mana sauki a wasu bangarorin Rayuwa, amma kuma sun zo da wasu hanyoyi na cutar da rayuwar dan Adam. Ga jerin matsaloli da wayar Zamani ta kawo a cikin Al’umma.

1. Yanke Dangantaka

Wasu zasu mamaki cewa wayar zamani ta yanke dandantaka bayan sukan da wasu ma ta sanadiyar ta suka hadu sukayi aure. Abunda nake nufi anan shine, tabbas wayoyin zamani suna bada dama kayi hulda da mutanen da baka taba sanin su ba, amma kuma matsalar itace muna nisantar na kusa damu. Aure da yawa ya mutu ta sanadiyar Shafukan Sada Zumunta kamar su Facebook whatsapp da sauransu.

2. Rayuwar Hoto

Jama’a da dama zasu yarda dani cewa a duk lokacin da mutun zai sayi waya zaka ga abu na farko da ake fara dubawa shine karfin Kamara (mega Pixel). Yanzu hada hotuna ya zama ruwan dare musamman ga Mata. Zaga yan mata wasu har da Yada tsirai cin su a Shafukan Sada Zumunta.

3. Daukar Lokaci

Binkice ya nuna abu na farko da na karshe da Mutane suke tabawa a yanzu shine wayar su. Da dama mutane na bata awa 10-12 suna kallon wayar su, Talabijin, ko Komfuta. Amma mafi yawancin awanin na a Yanar gizo ake bata su da buga wasanni (games).

4. Addictions

Sabon da Batsala wani wata babbar matsala ce da wayoyin zamani suka kawo cikin alumma, yarince da bata isa hira ba a gidan su amma waya zata bata dama ta rika waya da saurayi har abu ya kai ga ana aikawa juna hotunan da bai dace ba, ko kuma ka rika ganin bidiyo da hotuna (bluefim) da batsala a wayar yan mata da samari, wani lokacin har da magidanta. hakan nada nasaba da Wayar Salula na da sirri, sai ka aje irin wannan bidiyo da hotuna ba kowa ne zai san kana da su a waya ba. Ko kuma samari su rika bata yan mata, ba tare da sun je gidan su hira ba.

5. Dogaro da Kimiya da Fasaha

Yan mutane da dama zaga da akwai kalmomin da basu iya rubutawa saboda wayoyin salula suna gyarawa mutun kalmomi a lokacin da kake rubutu. Da zaka ga mutane da ka suke lissafi amma yanzu da an fara lissafi sai kaga an dauko waya domin anfani da abun lissafi(calculator). sannan kuma a koda yaushe cikin shiga Google ana tambaya yadda zaayi abu.

6. Matsaloli Ban Garen Lafiya

An fani da waya da Komfuta na kawo matsalar ciwon Baya, Ciwon Kai, Rashin isashen Barci, da Matsalar Ido.

Abunda nake so mu fahimta ana shine bawai waya ita kanta nada matsala bane yadda muke amfani da ita shine zai iya kawo matsalar da kan iya bata muna rayuwar mu.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-06-05 — 2:23 pm

3 Comments

Add a Comment
  1. Yahya Auwal Tsakuwa

    Gaskiya kam haka wannan magana take, illa iya ka dai mu muyi kokari muga munyi amfani da wayoyin hannunmu ta yanda Ya dace.

  2. mungode da irin wannan shawaran

  3. Gaskiya wannan bayanin yayi Allah dai yasa mu gane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme