MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Facebook Ya Kaddamar Da Wani Sabuwar Kimiya

Facebook ya kaddamar da wata sabuwar hanya da mutane zasu rika bayyanawa shugabannin da suka zaba na siyasa ra’ayoyinsu ta kafar Facebook.

Kamar yadda masu amfani da kafar Facebook ke rubutu su kafe, a cikin akwatin da suke rubutun an ‘kara wata sabuwar hanya da za ta taimakawa mutane wajen bincikar wakilan da suka zaba, su ‘kara bayanan su a rubutun.

Makasudin fitowa da wannan hanya shine domin mutane su bayyana ra’ayoyinsu da suka danganci harkokin siyasa ta kafar Facebook, haka kuma zasu iya yada ra’ayin da suka kafe domin mutane su karanta.

Ita dai wannan hanya yanzu haka masu amfani da kafar Facebook ta wayoyin hannu ko ta kwamfuta zasu iya amfani da ita. Sai dai kuma idan mutum ya rubuta ra’ayin na sa ba wai zai aikawa wakilin da ya rubutawa kai tsaye ba, amma sannu a hankali zai isa gareshi idan aka rubuta suna da mukami.

Fasaha ta baya-bayan nan da kamfanin Facebook ya fito da ita, itace kaddamar da hanyar da mutane zasu iya bincikar wakilansu na tarayya da jihohi da kuma na kananan hukumomi domin bibiyarsu ta kafar sadarwa.

daga Dandalinvoa.com

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-06-08 — 9:15 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme