MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Za Mu Ture Jarumai Irinsu Jamila Nagudu Da Hadiza Gabon Mu Kawo Sabbin Jini

Za Mu Ture Jarumai Irinsu Jamila Nagudu Da Hadiza Gabon Mu Kawo Sabbin Jini, Inji Darakta Aminu S. Bono

…yanzu harkar fim din Hausa ta masu ilmi ne, cewarsa

Daga Shazali Farawa

Shahararren mai bada umarnin nan ba finafinan Hausa Aminu S. Bono ya bayyana kalubalen da masana`antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood ke fuskanta da cewa karancin jarumai mata masu jinni a jiki.

A cewarsa masu kallon finafinan mu na yi mana kallon mahaukata idan muka sanya fuskokin jarumai mata irin su Hadiza gabon, Fati Washa, Aisha Tsamiyya, Jamila Naguda DS, amtsayin yan mata musamman ma na kauye, saboda yanzu fuskokinsu sun koma na iyeye ba yan mata ba.

Al`adarmu ta bahaushe ba ta yi daidai da ganin gandama gandaman yan mata irinsu a kauye ba a matsayin yan mata, saboda haka kallubalen masana`antar shine “newfaces”wato sabbbin jarumai masu tasowa irinsu Maryam Yahaya, Bilkisu Shema, Zulaihat Ibirahim,Zee Pretty, Amal Umar da sauransu.

“Amma yanzu jaruman da muke da su kamaninsu duk sun juye sun koma na tsofaffi kon kuma wasu iyaye, Sai dai matsalar mu da muka fuskanta a baya nada nasaba da karancin rashin hanyar fito da jaruman da za su maye gurbin tsofaffin da kullum masu kallon fuskarsu suka fara kosawa da su, saboda haka muka yi tunanin kawo sabbin jarumai ta hanyar da mutane suka fi so wato nishadi kamar ta hanyar wakokin bidiyo da ba a saba da su cikin finafinai ba.

“To kaga da wadannan wakoki muka siyar da fuskokin sabbin jaruman wanda yanzu kuma dukkaninsu sun samu daukaka da yardar Allah a wannan masana`anta, abin dake cimana tuwo a kwarya shine yadda har kullum masana`antar fuskokin wasu mutane kalilan ake kallo har masu kallo sun fara kosawa da hakan.

To kana ganin sanya fuskar sabbin jaruman a faifan bidiyon wakokin kwalliya tana biyan kudin sabulu?

Kwarai kuwa misali Garzali Miko, Maryam Yahaya, Amal Umar Abdul M. ShAriff da sauransu, dukkaninsu sun samu shiga domin kuwa masu kallon mu alkalan kansukan hakan , kuma gashi sun samu daukaka fiye da kima a masana`antar.

Shin fito da sabbin fuska ba zai kawowa finafinan nakasu ba, wajen kin karbuwa a kasuwa idan ba fuskokin da masu kallon suka saba gani ba kamar irinsu Jamila Nagudu?

Suma kafin su zo su Fati Muhammad ce tauraruwar su ke haskawa, kuma suma da suka zo ai cigaba aka samu saboda haka sababbin fuskoki a masana`antar shirya finafinan Hausa ta kannywood cigaba ne, duk lokacin da kakawo sabon abu akwai nasara a cikinsa musamman ma, sabon abun yazo da muradin abin da zaka sashi.

Bari in gayama wallahi idan fim ya grime ni bai fi da shekara daya ba. To bari ka ji da a masana`antar nan bama iya daukar jaruma mace sai masu zaman kansu amma suma duk da hakan idan mun je musu da bukatar su shigo fim kallon sana`ar suke da ta iskanci amma yau idan mata goma sun zo yin rajista za ka samu guda 7 cikinsu masu digiri ne ko kuma suna kan karatun.

“Yanzu sana`ar nan ta samu cigaba masu digiri ne ke shigowa masana`antar saboda nan gaba idan mutum baida ilimi bai isa ya shigo ba, mu kan mu yanzu kalubalen kenan da ya sanya mu komawa makaranta, nan gaba zamu ma ture marasa ilimi mu kawo masu ilimi.”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-06-27 — 9:05 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme