MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

RONALDO ZAI FARA SHIRIN FIM

RONALDO ZAI FARA FITOWA A SHIRIN FIM

Shahararren dan wasan kwallon kafa,Cristiano Ronaldo ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa,yana gaf da zama mashiryin fim.
A wannan karon,dan wasan wanda tuni tauraruwarsa ta haska a fannoni kamar su kwallon kafa,siyar da tufafi da kuma kasuwanci,zai rungumi sana’ar shirya fina-finai masu babuka wato Series a Turance
A cewar wani labari da aka wallafa a jaridar babbar masan’antar shirya fina-finai ta Hollywood ta Amurka,a fim din da Ronaldo zai shirya,za a nuna rayuwar wasu ‘ya ‘ya mata masu kwallon kafa wadanda suka fito da kasashe daban-daban.
Fitattun masu bada umarni a duniyar fina-finai, Liz Garci da Josh Harto ne za su yi ruwa da tsaki wajen tsara wannan shirin na Ronaldo.
Da yayi bayani a shafinsa na sada zumunta,Ronaldo ya ce,
“Kallon talabiji na daya daga cikin ababen da na fi sha’wa.Wannan fim da zan shirya tare da tallafin kwararru a fagen fina-finai na duniya,wata babbar dama ce a gare ni wajen shiga duniyar fina-finai wacce ni bakonta ne”.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-12 — 1:57 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme