KANNYWOOD: DAYA DAGA CIKIN FITATTUN JARUMAN KANNYWOOD ZATAYI AURE YAU

DAYA DAGA CIKIN FITATTUN JARUMAN KANNYWOOD ZATAYI AURE YAU

Daga Auwal M Kura
14/04/2018

A Yau Asabar , wato 14 ga Afrilu, 2018, za a ɗaura auren ɗaya daga cikin jarumai mata da ke Kaduna, wato Sadiya Kabala.
Za a ɗaura auren ta da sahibin ta mai suna Ahmad a masallacin Juma’a na Al-Mannar da ke Kaduna da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

Bayan ɗaurin auren kuma za a yi dina a wani otal mai suna Silver Sand da ke Titin Katuru, Unguwar Sarkin Musulmi.
To Allah ya sa a ce gara da aka yi, amin.

This website uses cookies.