MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD:Ban Taba Bude Facebook Ba Amma Wasu Na Amfani Da Sunana Don Bata Min Suna-Inji Sadiya Gyale

                Abinda Masu Yada Labaran Karya Keyi Yana Damuna-Inji Sadiya Gyale

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Fitacciyar Jarumar fina finan hausa na kannywood Sadiya Gyale,tace masu yin amfani da sunanta wajen yada jita jita akan labaran karya  suna matukar bata mata rai.

Ta bayyana haka ne a shirin ra’ayi riga na BBC hausa wanda aka gabatar ranar juma’a da al’muru kan yadda za’a magance yaduwar labaran karya.

A watan Yuli ne aka rika yada jita jita a kafafen sada zumunta cewa jarumar ta mutu a sabitin Malam Aminu Kano dake arewacin Njieriya.

Tun da nake bantaba bude facebook ba,amma yanzu idan ka shiga manhajar zaka samu account biyar ko sama da haka da suna amfani da sunana,kuma abin yana bata min rai saboda wasu mah sai kaga sun shiga roko.

“A lokacin azumin daya wuce naje saudiya sai wani ya rika amfani da sunana a facebook yana cewa wai naje wani wuri kudi sun yanke min don haka a taimaka min da kati na dubu kaza”

Gaskiya yadda ake amfani da sunana ana bata min suna yana damuna matuka”

Sadiya ta shaidawa BBC cewa,ita dai tana zaman zamanta da lafiyarta sai kawai taga anata kiranta a waya ana tambayarta ko lafiya don ga labarin dake yawo a kafafen sada zumunta.

“Tace tun tana daukar abin kamar wasa sai kuma taga cewa lallai an yada labarin cewa ta mutu

Tace labarin mutuwarta da aka yada yasa masoyanta da dama cikin tashin hankali,domin kuwa wasu daga cikinsu ko bacci kasa yi sukayi,wasu kuma a ranar ko abinci basu iya ci ba-inji ta”

Sadiya tace ita agaskiya labarin sam bai dameta ba,don kuwa a ranar ma bacci tayi har da mun shari.domin tasan cewa dukkan mai rai mamaci ne watarana.

Jaruma tace wadanda suka mutu ba gaggawa sukayi ba,haka wadanda suke raye ma ba jinkiri suka yiba,fatan Allah yasa ta cika da kyau da imani.

Sadiya ta kara da cewa a gaskiya yada irin wadannan labarai na karya sam ba daidai bane acikin al’umma musamman musulmai.

Tace..

“A gaskiya duk wanda ko wadda ta shirya wannan labarimto ta daukarwa kanta ko kansa babban alhaki kuma babu wata riba da mutum zai samu akan haka din”

Jarumar tace duk wanda ke fadar wane ya mutu ko wanceta mutu a hali karya ne.to ai Allah ne kadai yasan gawar fari,kuma ba mamaki ma shi mutumin dake yada irin wannan labarin shi ke kusa da rami.

Wacec Sadiya Gywale?

Tana daga cikin jaruman fina finan kannywood da sukayi fice musamman a tsakanin shekarun baya 2000 zuwa 2012

Ta fito a fina finai da sukayi fice kamar,Balaraba da Ikram da Qugiya,Tutar so da Kishiya ko ‘Yar uwa da kuma Kauna.

Tayi aure a shekarar 2015,amma kuma daga bisai sun rabu da mijin,bata fitowa acikin fina finan yanzu,ta fito a fina finai tare da jarumai kamar Ali Nuhu,da marigayi Ahmad S.Nuhu da Aminu Shariff Momo da dai sauran su.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-11 — 12:35 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme