MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: WASU BATA GARI SUN YIWA JARUMA ALIYU TSAMIYA KUTSE-KarantaKaji

                       Anyi Jaruma Aisha Tsamiya Kutse-Karanta Kaji

A labarin da Majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu keda samu na tabbatar da cewa an samu wasu bata gari da ba’a san ko suwaye ba,da suka yiwa jarumar nan ta wasannin fina finan hausa  na kannywood kutse a shafinta na dandalin sada zumunta Instagram.

Mun samu cewa yi mata kutsen keda wuya sai suka fara saka hotuna  da abubuwan da basu dace ba,tare da yunkurin yin amfani da sunanta wajen damfara da kuma rokon jama’a

Kamar yadda jaridar Legit.com ta ruwaito tace tuni dai jarumar ta canza wani asusun a dandalin mai adireshi kamar haka @Aishaaliyutsamiya tare da kuma sanarwa da jama’a musamman ma masoyanta da masu sha’awar fina finan ta haka.

Kafar dandalin sada zumunta ta instagram dai kafa ce da jaruman fina finan hausa ke amfani da ita musamman wajen ganawa da masoyan su,kuma jarumar na amfani da kafar sosai.

Ko a kwanakin baya an samu irin wadannan bata gari da suka bude shafi mai sunan jaruma Hadiza gabon inda suka fara yunkurin damfarar mutane da sunanta,kafin ta farga ta nesanta kanta da wanann shafi inda akarshe kuma tayi masu Allah ya isa.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-08 — 8:53 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme