MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

BABBAN YARON JARUMI ADAM A ZANGO HAIDAR YA ZAMA MAWAKIN HIP POP

Babban ɗan fitaccen jarumi Adam A Zango, mai suna Ali Haidar Zango, ya fara waƙar hip pop.

Za a riƙa yi masa laƙabi da “Star Boy”.

Ali, wanda aka fi sani da suna Haidar, da kan sa ne ya bayyana hakan a shafin sa na Instagram, inda ya sanar da mabiyan sa cewa waƙoƙin sa guda biyu su na nan fitowa da sunan ‘Godiya’ da kuma ‘Rayuwa’.
Ya kuma tura da saƙo inda ya bayyana cewa mahaifin sa ne ya gano basirar da Allah ya ba shi.
Haidar ya sha alwashin ba zai ba mahaifin nasa kunya ba a wannan aiki da ke gaban sa.
Mujallar Fim ta gano cewa har an kammala shirye-shiryen ɗaukar bidiyon wani ɓangaren na waƙoƙin matashin mawaƙin.

DUBA KAGA: ZAFAFAN HOTUNAN ADAM A ZANGO GUDA 10 DA SUKAYI FICE A SATIN NAN
Baban sa ya aika da wani guntun bidiyon waƙar Haidar ɗin a shafin sa na Instagram wadda ba ta wuce minti ɗaya ba.
A tattaunawar sa da mujallar Fim, Adam A. Zango ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ba a kammala aikin bidiyon waƙoƙin guda biyu ba, amma da zarar an gama za a sake su baki ɗaya, na gani da kuma na saurare.
Mutane da dama dai da man sun zura ido su ga yadda ɗan fitaccen jarumin zai kasance idan ya girma, kasancewar tuni dai an san makomar ‘ya’yan wasu fitattun jarumai irin su Ali Nuhu da Sani Danja, wanda kowa ya san ‘ya’yan su sun daɗe da fara fitowa a cikin finafinan Hausa.
Wasu sun riƙa hasashen inda ɗan gidan Zango zai karkata; shin mawaƙi ko makaɗi zai zama idan ya girma, ko kuwa shi ma jarumi zai zama kamar yadda sauran ‘ya’yan jarumai su ke zama jarumai su ma?
Sai dai shi Haidar an ga ya canza layi, inda ya bayyanar da kan sa a matsayin mawaƙi.
Ana ganin hakan ba abin mamaki ba ne, kasancewar baban nasa shi ma fitaccen mawaƙi ne.
Tun da farko Adam A. Zango da kan shi ya tura hotunan Haidar a Instagram, inda ya gabatar da shi ga mabiyan shafin sa su sama da 567,000. Haka kuma ya yi wa yaron addu’ar fatan alheri.
Ɗimbin yaran Zango ɗin, irin su Maryam Giɗaɗo, sun kwafi hotunan na Haidar sun wallafa a nasu shafukan na soshiyal midiya.
Haka kuma an buɗe wa yaron shafi nasa na kan sa a Instagram a ranar 5 ga Afrilu, 2018, wanda a cikin kwana biyar kaɗai har ya samu mabiya mutum 27,400.
Tun bayan rasuwar matashin mawaƙin hip pop Ameer Isah Hassan, wanda aka fi sani da Lil Ameer, an riƙa samun bayyanar yara ƙanana waɗanda su ka bazama cikin waƙoƙin na Ingausa.
Yanzu haka dai an samu ‘ya’yan ‘yan fim guda biyu waɗanda su ke hip pop, wato Sani TY Shaban da Ali Haidar Zango.
Wani abin la’akari kuma shi ne dukkan yaran kowanne ana yi masu laƙabi da wani suna kamar yadda al’adar hip hop ta ke. A yayin da ake kiran Sani TY Shaban da “Freii Boi”, shi kuma Haidar laƙabin sa shi ne “Star Boy”.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-06-07 — 3:40 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme