MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Category: MA’AURATA

KARANTA KAJI: DALILAI 10 DA YASA MATA KE BUKATAR YAWAN SADUWA DA MAZAJEN SU AKAI AKAI-Inji Wata Likita

Dalilai 10 Da Yasa Mata Ke Bukatar Yawan Saduwa Da Mazajen Su Akai-Akai –Likita – Kwararriyar Likita Maimuna Kadiri ta hori mata da su rika yawan saduwa da mazajen su domin samun annashuwa da karin kafiya a jikin su. Maimuna wadda ita ce babban likita kuma shugaban kanfanin (Pinnacle Medical Services) ta hori mata da […]

SOYAYYA A KASAR HAUSA

ramadan booth yayi aure

Soyayya wata aba ce mai qarfi da tasiri a zukatan jama’a, wanda ke kawo farin ciki da nutsuwa a tare da masu gudanar da ita. Qarfin soyayya kan iya kawo rikici da fitina wanda zai iya girgiza al’umma. A kan iya fadawa rikece-rikice ko yaqi a kan soyayya. Soyayya ita ce ke kawo zaman lafiya da cigaban al’umma. Ita kalmar soyayya ba wai ta tsaya bane tsakanin namiji ko mace, ta qunshi duk wata qauna dake tsakanin al’umma.

Malam Bello Sa’id a cikin littafinsa Dausayin Soyayya ya bayyana ma’anar So da “Qawa-zuci, ko tsananin qauna da buqatar kusanta ga wani mutum, ko wani abu daban.” Anan zamu iya tabbatar da haka a nau’in soyayya daban-daban. Misali Soyayya tsakanin da da mahaifi, ko jika da kakarsa ko miji da mata ko mutum da karansa, ko bawa da ubangijinsa da sauransu.

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme