MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ZA’A GINA CUCINA A SAUDIYA

WATA SABUWA:
ZA A GINA COCINA A SAUDIYA

#JaridarTarayya

Kafafan yada labarai na Masar sun rawaito cewa,shugabannin kasa mai tsarki sun kulla wata yarjejeniya da takwaroninsu na fadar Vatican da zummar gina cocina a Saudiyya don mabiya addinin Kirista shiyyar Katolika da ke kasar.
An sanar da cewa shugabannin na Saudiyya sun dauki wannan matakin don karya lagwan masu tsatssaucin ra’ayi da kuma yada kyamar addinin waninsu,wanda hakan ya haddasa wutar ta’addancin da kawo ya ki ci ya ki cinyewa a duniyar Islama.
Shugaban kungiyar Musulman duniya,Mohammed bin Abdul Karim Al-Issa da kuma mataimakin shugaban mabiyan addinin Krista shiyyar Katolika na Vatikan,fasto Jean-Louis Tauran ne suka rattaba hannu a wannan yarjejeniyar a birnin Riyadh na Saudiyya.
A ranar 14 ga watan Afrilun bana, Jean-Louis da tawagar Kiristocin Roma sun kai ziyara babban birnin Saudiyya don ganawa da yarima mai jiran gado na kasar,Muhammad Bin Salman.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-05 — 3:22 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme