MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WANDA YA TUBA DAGA ZUNUBAI, ZAI GA ZUNUBANSA RANAR ALKIYAMA?

WANDA YA TUBA DAGA ZUNUBAI, ZAI GA ZUNUBANSA RANAR ALKIYAMA
Tambaya:
Assalamu alaikum, tambayata ita ce mutum ne yayi ayyukan sabo kuma ya tuba tuba na gaskiya, shin ranar lahira Allah zai nuna masa wannan laifin ko kuwa tunda dai an yafe masa ba zai gan shi ba a lahira???
Amsa :
Wa alaikum assalam, a zahirin nassoshi wanda ya tuba daga zunubi tuba na gaskiya, kuma Allah ya amshi tubansa, ba zai gan shi ba ranar Alkiyama, saboda aya ta takwas a suratu Attahrim ta hada ingantaccen tuba da shiga aljanna, ‘yan aljanna kuma ba sa bakin ciki, yana daga cikin ka’idojin da malamai suka fada : Duk wanda ya tuba daga zunubi, ingantaccen tuba, to kamar wanda bai taba zunubi ba ne, abin da babu shi kuwa ba zai yiwu a gan shi ba.
Aya ta : 70 a suratul Furkan ta tabbatar da cewa: Wadanda suka aikata manyan zunubai, kuma suka tuba, Allah zai canza munanan aiyukansu zuwa kyawawa, Idan zunubai sun koma kyawawa, ta yaya kuma za’a gan su a muninsu ranar alkiyama ?
Allah ne mafi sani.
Dr . Jamilu Zarewa
12/04/2016

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-05-24 — 10:09 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme