MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

TAMBAYOYIN ADDININ ISALAMA , Daga SunnahNewsNigeria

JINI YA ZO MIN, BAYAN CIKINA YA KAI WATA BIYU ! !

Tambaya :
Assalamu alaikum, malam ya kokari malam tambayace gareni, na yi wata biyu ban ga al’ada ba, sai yanzu ta rinka zuwa tana daukewa, na zo asibiti sun ce juna biyu ne,to inya zo min da safe shikenan sai ya dauke sai kuma gobe da safe,sai in ya dauke inyi wanka in cigaba da sallah, malam to ko ya halatta hakan ?
Amsa:
To yar’uwa wannan jinin da kika gani mutukar yana kama da jinin hailar da kaki saba gani, to zai hana sallah, kuma zai dauki dukkan hukunce-hukuncen jinin haila, saboda asali duk jinin da ya zowa mace ana daukarsa a jinin haila, in dai ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma babu wani dalili a alqur’ani ko a sunna da zai hana shi ya zama haila.
A zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila, don haka duk yinin da ki ga jini to yana daukar hukuncin jinin haila ne , haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ki yi wanka duk yinin da ba ki ga jini ba, Saidai idan yana yayyankewa kusa-kusa, to kina iya jinkirta wankan, sai ki hada sallolin da ba ki ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa : “Bai sanya muku kunci a cikin addini ba” Suratu Hajj 78.
Don neman Karin bayani duba Almugni na Ibnu Khudaamah 1\214 da Dima’uddabi’iyya shafi na 11

Updated: 2018-05-31 — 5:47 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme