MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

TAFARKIN TSIRA: KARANTA KAJI TAMBAYOYI HUDU DA DAN ALJANNAH YASAN AMSAR SU-Daga Sheikh Aliyu Fantami

        Karanta Kaji: Tambayoyi Hudu Da Dan Aljannah Yasan Amsar Su-Daga Sheikh Aliyu Fantami.

Annabi (SAW) Ya ce idan mutum ya mutu, Mala’iku biyu za su zo masa sannan su masa tambayoyi hudu a ‘Kabarinsa. Wadannan tambayoyi sune:

(1) Waye Mahaliccinka?
Amsa: ALLAH.

2) Menene addininka?
Amsa: Addini na shine Musulunci

3) Me zaka ce akan wannan da
aka aiko muku?
Amsa: Muhammad, Manzon Allah

(4) Menene ilminka?
Amsa: Na karanta littafin Allah,
kuma na yi imani da shi.

Annabi (SAW) Yace duk wanda ya amsa ko ta amsa tambayoyin na dai dai a ‘Kabari, za a rubuta
sunansa/ta a cikin “ILLIYUN”
wanda shine register ta sunayen ‘yan Aljannah. (Abu Daud, 4753; Ahmad, 18063; Saheehul’Jamiy,
1676)
Yaa Allah ka ba mu ikon amsawa daidai da shiga wannan rajista mai daraja. Amin.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-07-29 — 1:32 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme