MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SUNNONI DA LADUBBA GUDA 17 NA RANAR IDI – MALAN NAFIU LABARAN TSAFE

*1-Yin ado da kwalliya dan ranar Idi. Saboda Hadisn Umar bin kaddhaba R.A. @ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 948 .

*2-Yin wankan ranar Idi kafin tafiya sallar idi* Ibn Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wankan idi. @ ﻣﻮﻃﺄ ﻣﺎﻟﻚ، 384 .
Sa’id bn Musayyib Allah yayi masa Rahama yana cewa:

*”Manyan sunnonin ranar Idi guda ukku ne tafiya masallacin idi a kasa da cin abinci kafin afita a idin karamar sallah da kamewa daga cin komai sai an dawo a babbar Sallah da yin wankan idi”* @ ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ ‏( 3/104 ‏) ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ

*3-Yin sallar idi kafin Huduba* Manzon Allah s.a.w da Abubakar da Umar sun kasance suna yin Sallar idi kafinvHuduba. @ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ – ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺼﻼﺓ – ﺗﻔﺮﻳﻊ ﺃﺑﻮﺍﺏ
ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ 972: ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻰ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻰ
ﺩﺍﻭﺩ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 1134 0

4-Haramunne yin Azumi a ranar Idi guda biyu, idan azumi da idin Layya*
Manzon Allah s.a.w yana cewa: *(Babu azumi a ranakun idi guda biyu,idin azumi da idin Layya)* @ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 1197

*5-Cin abinci ko wani abu kafin tafi sallar idin azumi,kuma anfi so aci dabino kuma aci mara sabanin Idan layya ana kamewa ba’acin komai sai an dawo daga Idi*

Manzon Allah s.a.w ya kasance baya tafi sallar idin azumi har sai yaci Dabino kuma yana cin dabinon ne mara. @ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 953 .

*6-Yin sallar Idi a musalla shine sunnah wato a bayan gari a wani fili ba masallaci ba*
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana fita musallane don yin sallar idi. @ ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 510 .
Ibn Umar R.A yana cewa: *”Manzon Allah s.a.w yana fitane da wuri zuwa musalla dan yin sallar idi….”* @ ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ، 1294

*7-Sunnane a fitar da mata da yara zuwa sallar idi,amma matan suyi shiga ta musulinci kuma kada su sanya turaren da kamshensa yake tashi* @ ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 511 .
Sayyadina Abubakar R.A yana cewa: *”Hakkine akan kowace budurwa da macen aure fita zuwa sallar idi”* @ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ .

*8-Tafiya masallacin idi kasa idan da ikon hakan* Manzon Allah s.a.w ya kasance yana tafiya masallacin idi akasa kuma ya dawo akasa. @ ﺣﺴﻦ / ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 1078 ‏( 1311 )
Aliyu bn Abi Dhalib R.A yana cewa: *”Yana cikin Sunnah tafiya sallar idi a kasa kuma aci wani abu kafin a fita idi”*. @ ﺣﺴﻦ / ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 530

*9-Chanza hanyar dawowa ko hanyar zuwa masallacin idi* Manzon Allah s.a.w ya kasance yana chanza haryar dawowa daga masallacin idi. @ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 986 .
Ibn Umar R.A yana cewa:
*”Na koya daga Manzon Allah s.a.w chanza har dawowa daga masallacin idi* @ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 254 .

*10-Yin kabarbari a ranar Idi,ana fara kabbarar ne daga farkon wanta zul-Hijjah har zuwa karhen yini na ranar 13 ga wata anayivson yawaita yin kabbarori akowane lokaci ba sai bayan sallah ba kadai*
Imam Sun’ãni yana cewa:
*”Yin kabbar tun daren idi har zuwa faravsallar idi yin hakan sunnane abisa haduwa mafi yawan malamai saboda farrasa fadin
Allah Madaukakin sarki*-
*( ﻭَﻟِﺘُﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻫَﺪَﺍﻛُﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ )* @ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 185
@ ﺍﻟﺼﻨﻌﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺳﺒﻞ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺍﻟﺠﺰﺀ ﺍﻟﺜﺎﻧﻲ : 101-100 .

11-Sigogin Kabbarorin ranar Idi* Daga Cikin sigogin da aka samo daga Sahabbai sun hada da;-
Siga ta farko;-
* ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺃﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ * @ ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ . ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ ( 3/125 ‏) ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ .
Siga ta biyu;-
* ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ *
Siga ta Ukku;- * ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻭﺃﺟﻞ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻫﺪﺍﻧﺎ . @ ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﺒﻴﻬﻘﻲ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ . ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ‏( 3/125 ‏) ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ

*12-Sanya Turare dan zuwa sallar idi* Abdillahi dan Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wanka ya sanya turare. @ ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ – ﺑﺎﺏ ﻣﺎ ﺭﻭﻱ ﻓﻲvﺍﻻﻏﺘﺴﺎﻝ ﻟﻠﻔﻄﺮ ﺣﺪﻳﺚ 015

*13-Ba’a sallar nafila kafin sallar idi ko bayanta,kuma ba’a kiran sallah ko iqama* @ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ – ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ 1517: @ ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ – ﺑﺎﺏ ﻣﺎﺭﻭﻱ ﺃﻧﻪ ﻻ ﺻﻼﺓ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻗﺒﻞ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻻﺑﻌﺪﻫﺎ ﺣﺪﻳﺚ 0143

*14-Yin gaisuwar sallah da fatan Alkhairi da fatan Allah ya maimata mana*
An samu daga aiyukan maganata suna yiwa junansu barka da sallah da fata alkhairi,daga cikin abinda suke fada akwai;- * ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ *

*15-Yin wasa na al’ada wanda babu sabon Allah acikinsa dan nuna farincin ranar Sallah,sannan mata zasu yi nasu wake da buda kayan kidansu na al’ada wanda babu sabon Allah* @ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ – ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ – ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ – ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺤﺮﺍﺏ ﻭﺍﻟﺪﺭﻕ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ – ﺣﺪﻳﺚ 921: ، ﻭﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ – ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ – ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻌﺐ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻣﻌﺼﻴﺔ ﻓﻴﻪ ﻓﻲ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ – ﺣﺪﻳﺚ 01527 :

*16-Cin wani abu daga cikin abinda ka yanka na layya bayan dawowa daga sallar Idi*
Manzon Allah SAW ya kasance baya cin abinci a idin babbar sallah har sai ya dawo daga Masallaci sannan yana fara cine daga wani sashe daga abinda ya yanka na layyarsa. @ ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ / 144.

*17-Girmama ranar Idin layya akan sauranvranaku domin ranace mai girma awajanvAllah*
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Mafi girman ranaku a wajan Allah sune; Ranar Layya da ranar washe garin Layya)*[email protected] ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ

Allah ne mafi sani

*Ina yiwa dukkan musulmai barka da sallah da fatan alkhair,Allah ya maimata mana* * ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-20 — 1:39 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme