MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SIFFOFIN MIJI NAGARI 15 DA KO WACE MACE KE BURIN AURE-KARANTA KAJI

                    Mijin Da Kowace Mace Ke So

Kamar yadda ba kowacce Mace Namiji ke so ba haka zalika ba kowana Namiji Mace ke so ba.
Akwai wasu siffofin nagari dake tattare da Mijin da kowacce macce ke so:

1.Mijin dake son matarsa bayan aurensu fiyeda yadda yake sonta a layi.

2.Miji mai kishin matarsa. Domin Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: “duk wanda baya kishin matarsa bazai shiga Aljannah ba”.

3.Mijin da ya dauki aure a matsayin Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin rayuwa kawai ba.

4.Wanda ya dauki matarsa a matsayin abokiyarsa, kanwarsa, almajirarsa, kuma abokiyar shawararsa.

5.Shine wanda baya zagin matarsa, baya cin mutuncinta, baya cin zalinta, baya ha’intarta koda a bayan idonta ne

6.Shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba cutarwa. Wanda idan ya fahimci halayen matarsa, yake hakurin zama da ita tare da kyautatawa domin neman rahamar Allah Ta’ala.

7.Shine wanda idan zai yi magana da matarsa, zai fadi gaskiya babu yaudara ko karya acikin zancensa.

8.Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewa: Iyayen matarsa, Iyayensa ne. ‘Yan uwanta ma ‘yan uwansa ne, kuma dangin matarsa danginsa ne.

9.Shine wanda yake daukar cewa farin cikin matarsa shine farin cikinsa kuma matsalar ta, itama tasa ce.

10.Shine wanda ke kokarin kiyaye sirrin matarsa, kuma yake kokarin kare mata mutuncinta koda a wajen ‘yan uwansa ne, tare da hikima da fahimtarwa.

11.Shine wanda baya fifita matarsa akan ‘yan uwansa, kuma baya tauye mata darajarta. Yana bawa kowanne gefe nasa hakkin kamar yadda shari’ah ta tanadar.

12.Shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da hakuri a cikin zuciyarsa domin kashe wutar tashin hankali da bacin rai a duk lokacin da hakan ta faru tsakaninsa da matarsa.

13.Shine wanda a kullum yake kokarin tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin Islama ba rayuwa irin ta yahudu da nasara ba.

14.Shine wanda yake zaune da matarsa komai dadi komai wuya ba zai dena nuna mata soyayya ba wai
don tafara yankwanewa ko kuma karfinta yafara raguwa.

15.Shine wanda yake bawa matarsa yabo a duk lokacin da tayi kwalliya ko kuma tayi girki komai rashin dadinshi. Miji nagari baya raki baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko gishiri yayi yawa. Sai dai yace: “uwargida abincin nan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri yayi mana shisshigi a ciki”

Allah Yasa mazaje su gane,su sauke hakkinsu na kulawa..Ameen

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-11-20 — 5:57 am

5 Comments

Add a Comment
  1. shema'u salis dirimin iya

    Allah yasa mudace kuma mu amfana ameen

  2. Abdulrazza Lawal Aliyu

    Allah yasa muzan mazaje nagari ga matayenmu.

  3. Allah yabamu nagari, ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme